Boka ne ya umarce an kashe mahaifiyata na kai masa sassan jikinta – Inji wani matashi

Boka ne ya umarce an kashe mahaifiyata na kai masa sassan jikinta – Inji wani matashi

Wani matashi dan shekara 29, Taiwo Akinola ya bayyana ma rundunar Yansandan jihar Legas dalilin daya sanya shi kokarin halaka mahaifiyarsa wanda ta haifeshi, Alice Iyabo, a cewarsa Boka ne ya uamrce shi, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Taiwo, wanda dan kungiyar asiri ne ta Aiye, kuma yana daga cikin masu damfarar mutane kudade ta hanyar amfani da yanar gizo da aka fi sani da suna Yahoo yahoo, ya nemi shawarar wani Boka ne akan yadda zai samu arziki.

KU KARANTA: Ana yiwa rayuwata barazana saboda siyasa – ‘Yar majalisa Maryam Bagel

Sai dai Bokan ya bayyana masa cewa lallai matukar yana son yin arziki sai ya kashe mahaifiyarsa ya kai masa wasu sassan jikinta, kamar yadda kaakakin rundunar Yansandan jihar, Chiker Oti ya bayyana.

Kaakakin yace wannan lamari mai muni ya faru ne a gida mai lamba 2 dake kan titin Raji Ajanaku, cikin unguwar Ayobo na jihar Legas, inda Taiwo ke zaune tare da Babarsa da jikanta mai suna Faruk.

“Zuwa yayi shagonta dake kusa da gidansu, inda ya kirata cikin daki da nufin zasu tattauna wani muhimmin magana, sa’annan ya kore jikan nata ta hanyar aikensa ya sayo masa hankici fari da karan sigari don kada ya ga abinda zai faru, shigarta keda wuya, sai Taiwo yah au dukanta da katako, dutsen guga har sai da ta fita hayyacinta.

“Da Faruk ya dawo, sai baiga kakarsa a shagonta ba, yayin daya shiga gida kuwa sai ya ganta kwance male male cikin jini, nan take ya saka ihu yana kuwwa, wanda hakan ya janyo hankulan makwabta, inda suka shigo don kawo masa dauki, ganin matar a kwance ya sanyasu kiran Yansanda, wanda suka kama Taiwo, sa'annan suka garzaya da ita Asibiti.” Inji Kaakakin.

Daga karshe Kaakakin yace Taiwo ya amsa laifinsa, kuma sun gano wasu kayan tsafe tsafe a dakinsa da kuma kan mutum, kuma yace kwamishinan Yansandan jihar ya biya kudin dubata ta.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel