2019: Duk da tarin Matsalolin Nigeria, Buhari ya cancanci a sake zabarsa -Sanata Sani

2019: Duk da tarin Matsalolin Nigeria, Buhari ya cancanci a sake zabarsa -Sanata Sani

- Buhari da APC sun cancanci a sake zabar su a 2019

- Akwai rikici a jam'iyar APC, musamman wajen salon shugabancinta

- Nasarorin da gwamnati mai ci a yanzu ta samu sun nunka matsalolin da kasar take fuskanta

Sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijai ta kasa, Shehu Sani, ya ce Shugaba Buhari da Jam'iyar APC sun cancanci a sake basu dama a zaben 2019, don ci gaba da jagorancin al'umar kasar.

Sanatan wanda ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidansa da ke Kaduna, ya ce, "Duk da irin irin tarin matsalolin da ke addabar Nigeria, gwamnati mai ci a yanzu karkashin shugaba Muhammadu Buhari ta yi matukar kokari wajen samar da ayyukan raya kasa"

Ya misalta shugaban kasa Buhari a matsayin wata alama ta nuna Gaskiya da jajircewa wanda nasarorinsa suka nunka matsalolin da kasar ke fuskanta.

KARANTA WANNAN: EFCC ta bawa wani Sanata goron Sallah ta hanyar maka shi a kotu

Har ila yau Shehu Sani ya tabbatar da cewa, "Zai zama abin kuskure da son kai idan muka rufe idanuwanmu muka ce babu wasu matsaloli da ake fuskanta a kasar nan, musamman a cikin shekaru uku da suka gabata. Akwai rikici a cikin jam'yar APC da matsaloli na shugabanci.

"Amma shugaban kasa Buhari yayi namijin kokari wajen samun kwarin guiwar yakar cin hanci da rashawa a tsakanin jami'an gwamnati, ya bunkasa tattalin arziki dama daga darajar kasar a idanun duniya.

"Gwamnati mai ci a yanzu ta kammala manyan ayyuka, tana kuma kan yin sabbi, yayin da rikicin yan tada kayar baya ya lafa sosai, a yau Nigeria tana cikin kwanciyar hankali fiye da lokutan baya" a cewar Sanatan.

Sai dai Shehu Sani ya yi nuni da cewa rashin aikin yi da talauci da yayiwa al'uma katutu abunda za'ayi jimami akansa ne, duk da ya ce nasarorin gwamnatin yanzu sun nunka matsalolin da kasar ke fuskanta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel