Dakaraun Sojin Najeriya sun yi ma mayakan Boko Haram kisan kiyashi a wata arangama

Dakaraun Sojin Najeriya sun yi ma mayakan Boko Haram kisan kiyashi a wata arangama

Dakarun rundunar Sojan sama sun yi watsa watsa da wani sansanin mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram a jihar Borno a kokarinsu na kakkabe ayyuka kungiyar daga yankin Arewa maso gabashin Najeriya, inji rahoton jaridar Daily Nigerian.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wani bidiyo da rundunar ta aiko mata ya nuna yadda jiragen yakin Sojoji suka yi luguden wutar azaba akan mayakan Boko Haram a sansaninsu dake Zanarai da Tunbun Rego, dukkaninsu a jihar Borno.

KU KARANTA: Ana yiwa rayuwata barazana saboda siyasa – ‘Yar majalisa Maryam Bagel

“Mun kaddamar da hare haren Zanari ne bayan mun yi muhimmin shiri sakamakon samun bayanan sirri dake nuna mayakan Boko Haram sun kafa sansani a kauyen a shirye shiryensu na kaddamar da hare hare akan Sojojin dake jibge a yankin tafkin Chadi.

“Nan da nan muka aika da jiragen yaki masu suna Alhpha Jet don yi ma mayakan na Boko Haram luguden wuta, cikin yan kankanin mintoci ya kashsu da dama, daga bisani muka aika da roka roka don gamawa da sauran da suka nemi tserewa.” Inji Kaakakin rundunar, Ibikunle Daramola.

Daga karshe Daramola yace rundunar ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen lalubo duk wani sansani na yan Boko Haram dake fadin gabashin Arewa gaba daya, tare da kashe su.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel