Gwamna Ganduje ya sallami Fursunoni 170 a jihar Kano

Gwamna Ganduje ya sallami Fursunoni 170 a jihar Kano

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito mun samu rahoton cewa, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayar da 'yanci na sallamar wasu fursunoni 170 dake garkame a gidajen kaso a fadin jihar.

Ganduje wanda ya shaidi wannan tagomashi na sallamar fursunonin daga gidan kaso dake Goron Dutse a yau Talata ya bayyana cewa, wannan kyautatawa wani bangare na tukwici gami da bayyana farin cikin babbar rana ta bikin babbar Sallah.

Gwamnan ya ci gaba da cewa, wannan lamari wani bangare na kudirin da gwamnatin tarayya ta sanya a gaba na rage cunkoso a gidajen kaso dake fadin kasar nan.

Gwamna Ganduje ya sallami Fursunoni 170 a jihar Kano

Gwamna Ganduje ya sallami Fursunoni 170 a jihar Kano

Ya ke cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayar da umarni ga dukkanin gwamnonin kasar a kan su agazawa gwamnatin sa wajen rage cunkoso a gidan yari dake fadin kasar nan, inda a halin yanzu gwamnatin Kano ta sallami kimanin fursunoni 200 tun kafuwar ta a shekarar 2015.

KARANTA KUMA: Ku tabbatar kun mallaki Katin Zaɓe a matsayin Makamin ku na ƙwatar 'Yanci - Sarkin Musulmi ga Matasa

A wannan hali da fursunoni ke bukatar kulawa ta gwamnati, gwamna Ganduje ya kuma gargadi akan sauya dabi'u da kasancewa mutane nagari tare da addu'ar tabbatuwar zaman lafiya a kasa nan.

Gwamnan ya kuma ba kowanen su N5000 a matsayin abin guzuri da za su rike a hannu yayin komawa ga 'yan uwan su.

Kazalika, wasu daga cikin fursunonin da suka samu 'yanci sun yabawa gwamnatin jihar dangane da wannan goma ta arziki tare da shan alwashi na kauracewa aikata miyagun laifuka a lokuta na gaba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel