Dalilin da yasa dole Saraki zai yi murabus daga kujerarsa - Gbajabiamila

Dalilin da yasa dole Saraki zai yi murabus daga kujerarsa - Gbajabiamila

Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai na tarayya, Femi Gbajabiamila ya ce dole ne shugaban majalisar dattawa Dr. Bukola Saraki ya yi murabus daga kujerarsa saboda a halin yanzu jam'iyyarsa ta PDP ba ta da rinjaye a majalisun wakilai da dattawa.

A wata hira da ya yi wa wakilin Premium Times, Gbajabiamila ya ce akwai banbanci tsakanin abinda ya faru da Tambuwal a lokacin da ya sauya sheka zuwa ACN wato jam'iyya maras rinjaye a wannan lokacin. Ya ce majalisar ta zabi Tambuwal ne ba jam'iyyar ACN ba.

Ya cigaba da cewa, Idan ma a wannan lokacin ya goyi bayan Tambuwal ya cigaba da kasancewa kakakin majalisar wakilai duk da cewa ya koma jam'iyya maras rinjaye, ba laifi bane ya canja tunaninsa idan ya samu karin haske daga doka.

Dalilin da yasa dole Saraki zaiyi murabus daga kujerarsa ta shugaban majalisa - Gbajabiamila

Dalilin da yasa dole Saraki zaiyi murabus daga kujerarsa ta shugaban majalisa - Gbajabiamila

"Yana daga cikin alamar nagarta idan mutum ya gane ya yi kuskure ya canja ra'ayinsa na baya. Ko kotun koli na tarayya tana zartar da hukunci kuma daga baya ta canja hukuncin idan ta gano akwai kuskure.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari zai bude katafaren sabon kamfanin giya a jihar Ogun

"Ina da kyayawan dangantaka da shugaban majalisar dattawa tun kafin in shiga siyasa, tare muka taso. Shi yasa wannan dambarwar da ta taso bata yi min dadi ba, da ma ba haka abubuwa suka faru ba. Baya ga maganan samun amincewan kashi biyu cikin uku na majalisa, ana duba munufar ko wace doka da ke kundin tsarin mulki.

"Idan doka bata yi bayani karara game da wani batu ba, sai a duba niyyar wanda suka rubuta dokar. Tambaya a nan shine, akwai wata hikima idan an bawa dan jam'iyya maras rinjaye shugaban cin majalisa?

"Amsar ita ce babu, domin idan aka bawa dan jam'iyya maras rinjaye shugabanci zai iya amfani da damarsa na shugaba wajen ganin cewa ya kuntatawa gwamnati ya hana ta gudanar da ayyukan da take bukatar yi.

"Zaiyi hakan saboda ya bawa jam'iyyarsa maras rinjaye damar karbe mulki daga gwamnati mai ci. Shi yasa babu wata hikima na baiwa dan jam'iyya maras rinjaye shugabancin majalisa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel