EFCC ta taso Sanatan da yaki komawa APC a jihar Akwa Ibom a gaba

EFCC ta taso Sanatan da yaki komawa APC a jihar Akwa Ibom a gaba

Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake yaki da masu yiwa tattalikin kasa zagon kasa watau EFCC a takaice ta shigar da kara a wata babbar kotu dake a garin Legas akan wani Sanata daga jihar Akwa Ibom game da almundahana ta wasu makudan kudade.

Kamar yadda muka samu Sanatan mai suna Albert Bassey EFCC na tuhumar sa ne da laifin ansar cin hancin motoci 12 da kudin su ya kai Naira miliyan 254 daga hannun wani dan kasuwa a lokacin yana kwamishinan kudi a jihar ta Akwa Ibom.

EFCC ta taso Sanatan da yaki komawa APC a jihar Akwa Ibom a gaba

EFCC ta taso Sanatan da yaki komawa APC a jihar Akwa Ibom a gaba

KU KARANTA: Mu kadai ne za mu iya kada Buhari a 2019 - Kwankwaso

Legit.ng ta samu cewa yanzu haka dai Sanata Albert Bassey shi kadai ne ya rage a jam'iyyar PDP a jihar biyo bayan ficewar sauran biyu da suka hada da Sanata Godswill Akpabio da kuma Nelson Effiong da suka koma APC a kwanan baya.

A wani labarin kuma, Tsohon ministan al'adu da yawon bude ido a Najeriya kuma dantakarar kujerar Gwamnan jihar Kuros Ribas a zaben 2019 mai zuwa Mista Edem Duke ya yiwa musulmai musamman Hausawa da fulani na jihar da ke zaune a garin Kalaba, sha-tara ta arziki.

Mista Duke, kamar yadda muka samu dai daga majiyarmu ya ba al'ummar ne dake a zaune a unguwar Bagobiri a cikin garin Kalaba, babban birnin jihar buhunnan siminti har guda 200 a matsayin gudummuwar sa ga masallacin da suke ginawa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel