Sarki Sanusi ya jagoranci Sallar Idi, ya yi Huɗuba kan Zaman Lafiya da Soyayyar Juna

Sarki Sanusi ya jagoranci Sallar Idi, ya yi Huɗuba kan Zaman Lafiya da Soyayyar Juna

Sarki Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi na Biyu, a yau Talata ya kirayi 'yan Najeriya akan su ci gaba ta wanzar da zaman lafiya a tsakankanin su tare domin kwanciyar hankali, soyayya da kuma hadin kan kasar Najeriya baki daya.

Sarkin na Arewa yayi wannan kira ne bayan jagorantar Sallah yayin gabatar da hudubar sa ga al'umma a farfajiyar Masallacin Idi na Kofar Mata dake tantagwaryar birnin na Kanon Dabo.

Ya jaddada bukata ga dukkanin 'yan Najeriya akan su kawar da bambance-bambancen addinai da siyasa wajen wanzar da zaman lafiya domin tabbatar da habaka ta tattalin arziki da kuma ci gaba a kasar nan.

Basaraken ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni a jihar akan tallafawa marasa hali da karamin karfi a wannan lokuta na neman yardar Mahalicci musamman yayin da wahalhalu na rayuwa ke ci gaba da matsantawa.

Ya kuma ce akwai bukatar al'ummar jihar su dage wajen gudanar da addu'o'i domin ci gaban ta musamman yayin da zaben 2019 ke ci gaba da karatowa.

Sarki Sanusi ya jagoranci Sallar Idi, ya yi Huɗuba kan Zaman Lafiya da Soyayyar Juna

Sarki Sanusi ya jagoranci Sallar Idi, ya yi Huɗuba kan Zaman Lafiya da Soyayyar Juna

A yayin da yake addu'ar samun albarkar noma a bana, Sarkin ya kuma nemi matasa marasa aikin yi akan su kauracewa zaman kashe wando domin dogaro da kawunan su da hakan zai tallafa wajen bunkasar ci gaba a kasar nan.

Sarki Sanusi ya kirayi al'ummar jihar akan su tabbatar da mallakar katin zabe kasancewar sa makami na samun dama ta kwatar 'yancin su yayin babban zabe na 2019, tare da gargadin su akan tsoron mahallacin su a dukkanin al'amurran su na rayuwa.

KARANTA KUMA: Buhari ya yi tafiya da ƙafafunsa ta tsawon mita 800 bayan halatar Sallar Idi a garin Daura

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje, Sanata Kabiru Gaya, Sanata Barau Jibrin, Kwamishinoni, 'yan Majalisar wakilai da kuma manyan makarrabai na fadar Sarki Kano.

Kazalika 'yan majalisar dokoki na jihar da kuma Hakimai daga kananan hukumomin 44 dake fadin jihar sun halarcin Sallar Idin, yayin da jami'an tsaro na hukumomi daban-daban suka mamaye harbar kamar yadda rahotannin suka bayyana.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel