Mu roki Allah ya kifar da Gwamnatin Buhari – Secondus

Mu roki Allah ya kifar da Gwamnatin Buhari – Secondus

Yayin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikawa ‘Yan Najeriya sakon goron sallah inda ya hakikance a kan batun maganin barayin kasar nan, a wani bangaren PDP ta fito ta yi na ta jawabin inda ta ke taya al’umma murna.

Mu roki Allah ya kifar da Gwamnatin Buhari – Secondus

Shugaban Jam’iyyar PDP ya nemi a roki Allah ya tika Buhari da kasa
Source: Depositphotos

Shugaban Jam’iyyar adawa na PDP na kasa Prince Uche Secondus yayi kira ga Musulman Najeriya su roki Ubangiji ya kawo masu dauki domin kauda Shugaba Buhari da Gwamnatin sa domin halin da ta jefa mutane a ciki tujn 2015.

Uche Secondus a jawabin da yayi a Ranar ja-ji-birin Sallah ya nemi Mutane su nemi Ubangiji ya kawo mafita ga wannan Gwamnatin Kasar. Shugaban PDP ya nemi Musulman kasar nan su yi amfani da damar idi su nemi mafita.

KU KARANTA: Ba zan bari a ci zarafin Buhari ba inji Yahaya Tango

Mun samu labari cewa Shugaban na PDP yayi wannan jawabi ne ta bakin Mai magana da yawun sa Ike Abonyi. Secondus ya kuma nemi jama’a su yi addu’o’i na musamman domin ganin an samu zaman lafiya da bunkasar tattali a Najeriya.

Jam’iyyar PDP tace abubuwa sun sukurkuce a kasar nan tun da Shugaba Buhari ya hau mulki don haka ake bikin sallah babu armashi. PDP tace ana buga mulkin kama-karya da kuma kashe jama’a game da rikicin siyasa da na tsaro a kasar.

Har wa yau, Jam’iyyar adawar ta nemi Jama’a da su cigaba da sa rai abubuwa za su gyaru musamman wajen ganin an yi zaben adalci a 2019. APC kuma dai tayi kira inda ya nemi jama’a su marawa Shugaba Buhari ya cika alkawarun sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel