Shugaban jam’iyyar APC na jihar Akwa-Ibom ya koma PDP

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Akwa-Ibom ya koma PDP

- APC ta kara rashin wani jigo zuwa jam'iyyar adawa

- Jam'iyyun biyu mafiya karfi a Najeriya na cigaba da musayar 'ya'yansu a kullum

- Masana siyasa na hangen haka matsalar sauya shekar zata kasance har zuwa lokacin zaben 2019

Shugaban jam'iyyar APC na jihar Akwa-Ibom Udoma Bob Ekarika ya fice daga jam'iyyar zuwa jam'iyyar PDP.

Guguwar sauyin sheka: Shugaban jam’iyyar APC na jihar Akwa-Ibom ya koma PDP

Guguwar sauyin sheka: Shugaban jam’iyyar APC na jihar Akwa-Ibom ya koma PDP

Ekarika wanda tsohon kwamishinan lafiya ne, ya bayyana komawar tasa zuwa jam'iyyar PDP a yayin wani taron gangamin marawa gwamna Udom Emmanuel baya domin sake tsayawa takara a karo na biyu, wanda aka yi a filin wasa Onna Township.

Ekarika ya ce "Na bar jam'iyyar da bata da wani amfani wadda ake kiranta APC, nayi alfaharin dawowata PDP. Kuma nan bada jimawa ba zan bayyana sirrin jam'iyyar".

Wasu daga cikin wanda suka fice daga jam'iyyar ta APC sun hada da mataimakin shugaban jam'iyyar Emmanuel Udoh, tare da Obong Ifiok Anny Asikpo, Emmanuel Francis Ikpe, Emmanuel Udofia, Obong Mbaba, Barr Anietie Etuk, Benedict Benjamin da kuma Amb George Ikpe.

KU KARANTA: Ihu bayan hari: Hadimai na sun yi murabus ne saboda ina shirin sallamar su - Gwamna Tambuwal

Shi ma daga bangarensa, guda daga cikin wanda suka fice daga jam'iyyar ta APC, Obong Asikpo ya bayyana APC a matsayin jam'iyyar mayaudara. Sannan ya kara da cewa zai yi kokari wajen ganin duk wani mutumin kirki ya fita daga jam'iyyar ya dawo PDP.

Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Akwa-Ibom Obong Paul Ekpo, a yayin da yake karbar sabbin ‘yan jam'iyyar, ya musu alkawarin za’a dama dasu kamar yadda ake bawa sauran ‘yan jam'iyyar dama.

"Muna muku maraba da dawowa jam'iyya mai kima, martaba da daraja, kuma ina mai muku alkawarin cewa za’a dama daku a duk wasu al'amuran da suka shafi jam'iyyar nan".

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel