Saboda dakon mulki Tinubu yake bayan Shugaba Buhari – Inji Saraki

Saboda dakon mulki Tinubu yake bayan Shugaba Buhari – Inji Saraki

Mun ji labari cewa Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya maidawa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu martani bayan tsohon Gwamnan Legas din ya zargi Saraki da harin kujerar Shugaba Buhari.

Saboda dakon mulki Tinubu yake bayan Shugaba Buhari – Inji Saraki

Bukola Saraki ya fede babban Jigon Jam’iyyar APC Bola Tinubu

A makon nan ne Bola Tinubu ya bayyana cewa Bukola Saraki da Aminu Tambuwal sun fice daga APC ne domin su na neman kujerar Shugaban kasa. Saraki ya fito ya kare kan sa duk da yace bai so ya rika maidawa Tinubu martani ba.

Bukola Saraki a wannan dogon jawabi da yayi jiya ya bayyana cewa Bola Tinubu ya fada masa cewa ko Shugaba Buhari yana mulki kan kujerar katako ne za su cigaba da mara masa baya domin mulki ya dawo Kudu bayan zaben 2019.

KU KARANTA: Abin da ya sa su Tambuwal su ka koma PDP - Tinubu

Shugaban Majalisar Kasar yace Bola Tinubu ya fada masu wannan ne da bakin sa a wata ganawa inda yace Tinubu su na tare da Buhari ne ba don yana kokari a karagar mulki ba, sai dai don kurum mulki zai dawo hannun Yarbawa a 2023.

Kwanakin baya ne dai Bukola Saraki ya fice daga APC ya koma Jam’iyyar PDP wanda hakan ya sa Tinubu yace gigin shugabancin kasar nan ke damun Saraki. Saraki dai ya karyata wannan inda yace kishin kasa ya sa gaba ba komai ba.

Shugaban Sanatocin kasar dai yace Tinubu na neman kashin muyar sa ne da zarar Shugaba Buhari ya kammala wa’adin sa. Shi ma Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal yace Tinubu yayi kokarin jefa APC a matsala saboda kujera a 2015.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Mailfire view pixel