Sai Najeriya tayi shekaru 10 ba ta farfado ba idan Atiku ya mulke ta na kwana daya - Okupe

Sai Najeriya tayi shekaru 10 ba ta farfado ba idan Atiku ya mulke ta na kwana daya - Okupe

Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Dr Doyin Okupe ya ce muddin aka sake aka zabi tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a matsayin shugaban Najeriya za'a samu koma bayan da za'a kwashe shekaru 10 ba'a farfado ba.

Atiku Abubakar yana daya daga cikin masu neman kujerar takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP a zaben shekarar 2019 mai zuwa.

Sai dai Okupe wanda shine tsohon mai magana da yawun tsohon shugaban kasa Jonathan ya ce bai dace a bawa Atiku damar mulkar Najeriya ba.

Sai Najeriya tayi shekaru 10 ba ta farfado ba idan Atiku ya mulke ta na kwana daya - Okupe

Sai Najeriya tayi shekaru 10 ba ta farfado ba idan Atiku ya mulke ta na kwana daya - Okupe

Atiku ya kasance mataimakin tsohon shugaban kasa Obasanjo tsakanin 1999 zuwa 2007.

DUBA WANNAN: Obasanjo ya lissafa nasarorin da sabuwar jam'iyyar ADC ta samu cikin kankanin lokaci

Kamar yadda ta wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Litinin, Okupe ya ce idan aka zabi shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki a matsayin shugaban kasa, zai daura Najeriya kan turbar cigaba kuma zai kafa tarihi.

A yammacin Litinin din, Okupe ya wallafa shafinsa na Twitter, "Idan Atiku ya mulki Najeriya na kwana 1 tak, Najeriya zata shafe shekaru 10 kafin ta farfado. Idan Saraki ya mulki na rana 1, Najeriya zata kafa tarihi."

Idan mai karatu bai manta ba, Okupe yana daya daga cikin wadanda ba 'yan majalisa ba da suka hallarci taron manema labarai na Saraki ya kira kwana daya bayan jami'an 'yan sandan farin kaya DSS sun hana shiga majalisar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel