Ihu bayan hari: Hadimai na sun yi murabus ne saboda ina shirin sallamar su - Gwamna Tambuwal

Ihu bayan hari: Hadimai na sun yi murabus ne saboda ina shirin sallamar su - Gwamna Tambuwal

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato ya yi ikirarin cewa mataimakansa na musamman da masu bashi shawara guda 250 da su kayi murabus sunyi aikata hakan ne saboda sun san yana da niyyar korarsu.

Direkta Janar na Kafefen yada labarai da ayyukan jama'a na gwamnan, Malam Abubakar Shekara ne ya bayar da wannan sanarwan a daren Lahadi.

Ya ce Tambuwal ya riga ya bayar da umurnin sallamar dukkan masu taimaka masa na musamman daga aikinsu a jihar.

Ihu bayan hari: Gwamna Tambuwal ya ce hadimansa da su kayi ajiye aiki dama yana nufin koransu

Ihu bayan hari: Gwamna Tambuwal ya ce hadimansa da su kayi ajiye aiki dama yana nufin koransu

DUBA WANNAN: Bikin Sallah: Gwamna Tambuwal ya yiwa marayun Sakkwato sha tara na arziki

Ya ce gwamnan ya dauki matakin ne domin ya basu damar gudanar da harkokin siyasarsu ba tare da wata tangarda ba saboda kasancewarsu hadimansa.

Sai dai hadiman gwamnan sunce sunyi murabus ne daga ayyukansu saboda sauya sheka da gwamnan ya yi daga jam'iyyar APC zuwa PDP. Sun kuma zargi gwamnan da rashin tabuka wani aikin azo a gani a jihar.

Sai dai duk da hakan, wasu tsaffin masu bayar da shawara na musamman da mataimaka na musamman na gwamna Tambuwal sun jadada goyon bayansu gareshi da jam'iyyar PDP da ya koma.

Daya daga cikinsu, Alhaji Nasiru Shamaki wanda shine tsohon sakataren kungiyar masu taimakawa gwamnan na musamman ya ce wadanda su kayi ikirarin suyi murabus makaryata ne domin gwamnan ya riga ya sallami dukkan mataimakansa na musamman da masu bashi shawara a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel