Hadama: Babban wa ya yanka kannensa biyu da aka mutu aka bar su tare

Hadama: Babban wa ya yanka kannensa biyu da aka mutu aka bar su tare

An shiga halin firgici da dimuwa a kan titin Summit dake garin Asaba a jihar Delta biyo bayan kisan wasu yara biyu – Kingsley Nwani da Nwayo Nwani – da yayansu Aniemeka Nwani ya yi.

Wata majiya ta bayyana cewar yayan nasu ya dauki wani mummunan mataki ne a kan kannen nasa bayan an dauki lokaci mai tsawo suna rikici a kan kadarar da mahaifinsu yam utu ya bari.

Lamarin ya faru ne a a jiya, Litinin, a wani gidan man fetur da mahaifinsu yam utu bari kuma kannen nasa ke kula da shi.

Daya daga cikin kannen nasa, Kingsley, take yam utu bayan Aniemeka ya yi masa rauni da wuka yayin da dayan, Nwayo, yam utu a asibiti inda ake kokarin ceton ran sa.

Hadama: Babban wa ya yanka kannensa biyu da aka mutu aka bar su tare

Babban wa ya yanka kannensa biyu da aka mutu aka bar su tare

Majiyar jaridar Punch ta shaida mata cewar tun kafin mutuwar mahaifinsu Kingsley da Nwayo ke kula da gidan man fetur din.

Sai dai bayan mutuwar mahaifin nasu, yayansu, Aniemeka, ya yi kokarin su damka gidan man fetur din a hannunsa amma suka ki. Hakan ya saka shi daukan wannan danyen hukunci.

DUBA WANNAN: 'Yan bndiga sun kashe malamin addini, sun sace matar sa a Kaduna

Yanzu haka dai Aniemeka ya cika wandonsa da tsoka bayan ta’asar da ya tafka.

Ba a samu jin ta bakin Andrew Aniamaka, kakakin hukumar ‘yan sanda ta Delta ba, amma wani jami’in hukumar a jihar ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel