Dalilin da yasa Saraki da Tambuwal ke fushi da Tinubu - Onuchie

Dalilin da yasa Saraki da Tambuwal ke fushi da Tinubu - Onuchie

Mai taimakawa shugaba Buhari a fannin kafafen sada zumunta, Lauretta Onochie, ta ce Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, suna fushi da Shugaban APC na kasa, Cif Bola Ahmed Tinubu ne saboda baya fargaban fadin gaskiya.

Ta ce Saraki da Tambuwal sun dogara ne da rahotannin bogi da jam'iyyar PDP ta biya kamfanin tattara bayanan sirri na Cambridge Analytica game da rashin lafiyar shugaba Buhari sai dai gashi har yanzu lafiya kalau yake.

Dalilin da yasa Saraki da Tambuwal ke fushi da Tinubu - Onuchie

Dalilin da yasa Saraki da Tambuwal ke fushi da Tinubu - Onuchie

DUBA WANNAN: Bikin Sallah: Gwamna Tambuwal ya yiwa marayun Sakkwato sha tara na arziki

Onuchie ta ce a halin yanzu 'yan Najeriya sun kashi gida biyu, akwai wadanda suka amince da yaki da rashawa da shugaba Buhari keyi kamar yadda APC ke bayyanawa sannan akwai bangaren da kullum cewa su keyi rashawa na karuwa kamar yadda PDP ke bayyanawa.

Ta shawarci 'yan Najeriya su goyi bayan yaki da rashawa da Buhari keyi domin babu wani gwanin yaki da rashawa kamarsa a Afirka.

"Buhari ne alhakin da ya fadawa masu satar kudaden talakawa.

"Shine gwanin da ke kare wadanda aka dade ana zalunta, shine wanda zai kwatowa marasa galihu hakkinsu." inji Onuchie.

Daga karshe Onuchie ta yi kira ga jama'ar jihar Kwara su zaburo domin kare kansu da iyalansu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel