Saraki ya bayyana dalilin da ya sanya Tinubu ke goyon bayan Buhari

Saraki ya bayyana dalilin da ya sanya Tinubu ke goyon bayan Buhari

Shugaban Majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki, ya bayyana babban dalilin da ya sanya kanwa uwar gamin matsalolin jam'iyyar APC watau Asiwaju Bola Tinubu, ke ci gaba da goyon bayan shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Saraki ya bayyana cewa, Tinubu na ci gaba da goyon bayan zarcewar shugaba Buhari a karo na biyu yayin zaben 2019 domin ya ci gajiyar kujerar a shekarar 2023.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, Saraki ya bayyana wannan zargi cikin wata sanarwa a ranar Litinin din da ta gabata dangane da martani kan wata budaddiyar wasika da Tinubu ya rubuta a ranar Lahadin da ta gabata.

Tinubu cikin budaddiyar wasikar sa ya bayyana cewa, Shugaban majalisar dattawan ya yi watsi da jam'iyyar APC ne kadai domin cimma manufar sa ta neman kujerar shugaban kasa da ba ta da wani tushe face na son zuciya.

Saraki ya bayyana dalilin da ya sanya Tinubu ke goyon bayan Buhari

Saraki ya bayyana dalilin da ya sanya Tinubu ke goyon bayan Buhari

A yayin da aka baiwa Tinubu ragama ta kanwa uwar gamin matsalolin jam'iyyar APC, ya bayar da shaidar cewa ko kadan ba ya alfahari gami da rashin gamsuwa dangane da yanayi na jagorancin shugaba Buhari, amma haka zai ci gaba da jajircewa wajen goyon bayan sa domin samun dama ta cin gajiyar kujerar sa a shekarar 2023 kamar yadda Saraki ya bayyana.

KARANTA KUMA: Jahohin Najeriya 6 da suka fi ko ina yawan musulmai

Saraki ya kuma yi fallasa ta cewar Tinubu ya tabbatar ma sa da goyon bayan Buhari maras yankewa koda kuwa zai ci gaba da mulkin kasar nan a kan gadon jinya.

Shugaban majalisar ya kara da cewa, ya fice daga jam'iyyar APC ne kadai sakamakon walakantaswa da shugaba Buhari ke yiwa Majalisun dokoki na gwamnatin kasar nan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel