Mutane 3 sun sheka lahira yayin karon-batta tsakanin magoya bayan jam'iyyar APC da PDP

Mutane 3 sun sheka lahira yayin karon-batta tsakanin magoya bayan jam'iyyar APC da PDP

- Bangar siyasa ta yi sandin mutuwar magoya bayan 'yan siyasa

- Hargitsi ya barke ne yayin da aka so kaiwa kantoman karamar hukumar Brass ta jihar Anambra

A kalla mutane uku ne suka mutu a wani karon-batta da magoya bayan jam'iyyar APC dana PDP suka yi jiya a karamar hukumar Brass dake jihar Anambra.

Amma sai jami'an 'yan sanda na jihar sun bayyana rasuwar mutum daya ne kawai a rahotansu.

Mutane 3 sun sheka lahira yayin karon-batta tsakanin magoya bayan jam'iyyar APC da PDP

Mutane 3 sun sheka lahira yayin karon-batta tsakanin magoya bayan jam'iyyar APC da PDP

Sai dai magoya bayan jam'iyyar PDP sun ce mutune uku ne suka rasu sakamakon harin da aka so akai kan mai rikon kwaryar karamar hukumar Brass Victor Isaiah ne.

KU KARANTA: Laifin majalisa ne zalla kin amincewa da kasafin kudin hukumar zabe – Fadar shugaban kasa

Sai dai magoya bayan jam'iyyar APC sun ce an kawo wasu mutane ne wanda ba yan asalin karamar hukumar ba, don su tada zaune tsaye. Wanda daga bisani suka far musu da Adduna da kuma bingidu.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Asinim Butswat ya ce "An samu barkewar fada tsakanin wasu matasa da suka ce su magoya bayan APC da PDP ne".

"Mutum daya ya rasu, sai guda biyu da suka ji rauni. Kuma ya zuwa yanzu an kai jami'an tsaro yankin domin tabbatar da tsaro". Kakakin 'yan sandan ya shaida.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel