Bikin Sallah: 'Yan sandan Najeriya sun bankado wata kullalliyar tada zaune tsaye a Arewa

Bikin Sallah: 'Yan sandan Najeriya sun bankado wata kullalliyar tada zaune tsaye a Arewa

Jami'an 'yan sandan Najeriya dake a jihar Kwara ta Arewa ta tsakiyar Najeriya ta sanar da samun nasarar bankado wata kullalliya ta tayar da yamutsi a wajen bikin shagulgulan babbar sallah a garin Iloli, babban birnin jihar.

'Yan sandan haka zalika sun bayyana cewa a sabo da hakan ne ma yasa suka baza jami'an su har 2,500 domin su bayar da tsaro da kariya ga alummar garin.

Bikin Sallah: 'Yan sandan Najeriya sun bankado wata kullalliyar tada zaune tsaye a Najeriya

Bikin Sallah: 'Yan sandan Najeriya sun bankado wata kullalliyar tada zaune tsaye a Najeriya

KU KARANTA: Tun da na bar APC nike fuskantar matsaloli = Inji wani gwamna

Legit.ng ta samu cewa haka zalika 'yan sandan sun tara 'yan siyasar jihar inda suka tilasta masu sa hannu a wata takardar yarjejeniya ta alkawarin zaman lafiya.

A wani labarin kuma, Fitaccen dan siyasar nan daga Arewacin Najeriya, Sanata kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa dan takara daga Arewa maso yammacin Najeriya ne kawai zai iya kada Buhari a zaben 2019.

Kwankwaso ya fadi hakan ne a lokacin da yake yiwa 'yan jam'iyyar sa ta PDP jawabi a garin Benin na jihar Edo a cigaba da rangadin da yake yi a game da batun takarar sa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel