Mu kadai ne za mu iya kada Buhari a 2019 - Inji Kwankwaso

Mu kadai ne za mu iya kada Buhari a 2019 - Inji Kwankwaso

Fitaccen dan siyasar nan daga Arewacin Najeriya, Sanata kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa dan takara daga Arewa maso yammacin Najeriya ne kawai zai iya kada Buhari a zaben 2019.

Kwankwaso ya fadi hakan ne a lokacin da yake yiwa 'yan jam'iyyar sa ta PDP jawabi a garin Benin na jihar Edo a cigaba da rangadin da yake yi a game da batun takarar sa.

Mu kadai ne za mu iya kada Buhari a 2019 - Inji Kwankwaso

Mu kadai ne za mu iya kada Buhari a 2019 - Inji Kwankwaso

KU KARANTA: Hadiman Gwamna Tambuwal 252 sun yi murabus

Legit.ng ta samu cewa dai tun farko jam'iyyar ta PDP ta ce dan takarar ta zai fito ne daga yankin Arewacin kasar amma ba tare da yin togacciya ba ga bangaren Arewa maso yammacin kasar da daga nan ne shugaba Buhari ya fito shima.

Jahohi bakwai ne dai suka hadu suka hada shiyyar Arewa maso yamma da suka hada da Kano, Kaduna, Katsina, Sokoto, Kebbi, Zamfara da kuma Jigawa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel