2019: Babban basarake a jihar Kwara ya yi watsi da Saraki, ya goyi bayan Buhari

2019: Babban basarake a jihar Kwara ya yi watsi da Saraki, ya goyi bayan Buhari

Wani babban basarake a jihar Kwara, Etsu Patigi, Alhaji Ibrahim Chatta-Umar, ya shiga sahun ayarin matasan karamar hukumar Patigi ta jihar Kwara wajen nuna goyon bayansu ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019.

A jiya, Lahadi, ne dumbin matasa a karamar hukumar ta Patigi suka gudanar da wani taron gangami domin nuna goyon bayansu ga takarar shugaba Buhari tare da bayyana cewar basa tare da shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, duk da kasancewar sa tsohon gwamna a jihar Kwara.

2019: Babban basarake a jihar Kwara ya yi watsi da Saraki, ya goyi bayan Buhari

Saraki da Buhari
Source: Depositphotos

Matasan da suka yi taron sun yi tattaki ya zua fadar sarkin domin bayyana masa goyon bayansu ga takarar shugaba Buhari. A nasa jawabin, Mai martaba Chatta-Umar, ya bayyana cewar da shi da jama’ar sa basu da dan takarar da zasu kadawa kuri’a idan ba shugaba Buhari ba.

DUBA WANNAN: Zunubai 6 da suka zubar da mutuncin Saraki a idon 'yan Najeriya - APC

A satin da ya gabata ne shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya sanar da wata jarida, Bloomberg, cewar yana tuntuba tare da bayyana cewar yana da niyya mai karfi ta yin takarar shugaban kasa.

A nata bangaren, jam’iyyar APC ta mayar da martini ga wannan buri na Saraki tare da kalubalantar sa cewar ba shi da kimar da ‘yan Najeriya zasu zabe shi a matsayin shugaban kasa saboda wasu zununai da ta lissafa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel