Jam’iyyar APC tayi watsi da wasu kusoshin siyasa bayan 2015 – Lasun

Jam’iyyar APC tayi watsi da wasu kusoshin siyasa bayan 2015 – Lasun

Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilan Tarayya Najeriya Honarabul Lasun Yussuff ya koka da tafiyar da ake yi a Jam’iyyar APC mai mulki inda yace an maida wasu saniyar ware a Jam’iyyar bayan an ci zabe.

Jam’iyyar APC tayi watsi da wasu kusoshin siyasa bayan 2015 – Lasun

Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai yace akwai matsala a APC

Lasun Yussuff wanda ke wakiltar Yankin Osogbo/Olorunda/Orolu/Irepodun na Jihar Osun da yake hira da ‘Yan jarida a Garin Osugbo ya bayyana cewa APC tayi watsi da wasu manyan ‘Yan siyasa tun bayan da aka kafa Gwamnati.

Lasun ya bayyana cewa ba zai bar APC ba duk da abin da yake faruwa inda ya sha alwashin ganin Jam’iyyar sa tayi nasara a zabe mai zuwa. Hon. Lasun yace za su marawa wanda APC ta tsaida baya a zaben Gwamna nan gaba.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya wuce Daura domin bikin Sallah

Yusuff Lasun ya kuma bayyana cewa a lokacin da ya zama Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai babu wani a Gwamnati ko cikin Jam’iyyar APC da ya taya sa murna. A Satumba ne za ayi zaben Gwamna a Jihar Osun.

‘Dan Majalisar ya bayyanawa jama’a cewa akwai matsala a yadda ake gudanar da sha’anin Gwamnati a mulkin APC amma yace hakan ba zai sa su fita ba. Gboyega Oyetola ne zai yi takarar Gwamna a karkashin Jam’iyyar APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel