Yan sanda sun damke matashin da yayi yunkurin kashe mahaifiyarsa

Yan sanda sun damke matashin da yayi yunkurin kashe mahaifiyarsa

Hukumar yan sandan a jihar Legas sun damke wani matashi dan shekara 29, Taiwo Akinola, da laifin kokarin kashe mahaifiyarsa a Unguwar Ayobo da ke jihar.

Hukumar yan sandan ta samu kira ne daga makwabta wadanda suka ga yadda ya fasa kan mahaifiyarsa mai suna, Alice Akinola.

Game da cewa hukumar, matashin na zama ne da mahaifiyarsa da jikanta mai suna Faruk.

Jawabin yan sandan yace: “A wannan rana, Taiwo ya shiga shagon mahifiyarsa ya fada mata yana son tattaunawa da ita kan wani batu mai muhimmanci. Sannan ya aiki jikanta, Faruk, yasayo masa sigari da zanen aljihu.”

“Shigan mahaifiyarsa ke da wuya, sai ya buga mata katako a kai sannan da dutseun guga domin ganin cewa ya kasheta.”

“Amma asirinshi ya tonu yayinda yaron da ya aika Faruk ya dawo. Ya shiga shago amma bai ganta ba, sai ya shiga cikin gida inda ya ganta cikin jinni. Wannan abu ya bashi tsoro sannan ya sanar da makwabta.”

KU KARANTA: Magoya bayan Buhari da Saraki sun yi arangama a filin jirgin Ilori

Yayinda binciken da hukuar ta gudanar, matashin ya tabbatar da cewa shi dan kungiyar asiri ne kuma ya yi niyyar kashe mahaifyarsa ne domin bunkasa aikinsa na damfarar yanar gizo.

An kai mahaifiyar asibiti inda likitoci ke kokarin ceto rayuwarta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel