Hukumar EFCC ta yi ram da hadimin Saraki kan badakalar N3.5bn

Hukumar EFCC ta yi ram da hadimin Saraki kan badakalar N3.5bn

- Karan EFCC ya yiwo kan babban hadimin shugaban majalisar dattawa

- Ana zarginshi da karkatar da makudan kudin jihohi

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta shirya gurfanar da Gbenga Makanjuola, mataimakin shugaban ma’aikatan shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da tsohon manajan bankin Societe Generale Bank of Nigeria( SGBN), Mr. Robert Mbonu.

Za’a gurfanar da sun biyun kan karkatar da kudi N3.5billion daga cikin N19billion na London-Paris Club

Sauran da ake zargi sune Melrose General Services Limited da Obiora Amobi. Har yanzu dai bai ayyana ranan da za’a gurfanar da sub a a babban kotun tarayya da ke Legas.

KU KARANTA: Hukumar NECO ta fitar da sakamakon jarabawar SSSCE ta 2018

Bisa ga kukan da jihohi sukayi na kudadensu d gwamnatin tarayya ta rike tsakanin shekarar 1995 zuwa 2002, shugaba Muhammadu Buhari ya bada izinin baiwa gwamnonin N522.74bn a matsayin biyansu hakkinsu.

Kowace jiha tanada hakkin N14.5billion, wanda kasha daya cikin hudun da aka rike musu ne.

Hukumar EFCC ta yi ram da hadimin Saraki kan badakalar N3.5bn

Hukumar EFCC ta yi ram da hadimin Saraki kan badakalar N3.5bn

A shekaru biyu da suka gabata, hukumar EFCC batayi kasa a gwiwa tana binciken karatar da N19bn da sunan kudin dillalai da aka baiwa kamfanin Melrose General Services Limited.

Kimanin kudi $183,000 wasu sanatoci suka turawa wani mai sayar da gwala-gwalai a kasar Dubai.

Da aka gudanar da bincike, an samu cewa babu aikin dillancin da kamfanin tayi da aka biyata maudan kudi har N3.5bn.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel