Rundunar soji ta karyata cewar yan Boko Haram sun kashe jami’anta

Rundunar soji ta karyata cewar yan Boko Haram sun kashe jami’anta

Rundunar sojin Najeriya ta karyata rahotannin kafafen yada labarai dake cewa ta rasa sojoji sama da 50 ga yan ta’addan Boko Haram.

Rundunar tace rahoton wanda ta bayyana a matsayin karya ya kasance daya daga cikin hanyoyi da dama da yan ta’addan Boko Haram ke amfani das u domin yaudarar jama’a daga nasarar da sojoj suka yi akan su.

Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgadier Janar Texas Chukwu da yake martani ga rahoton yace lallao sojojin dake arewa maso gabas na nan cikin lafiya, inda ya bukaci yan Najeriya da kada su yadda a kanzon kuregen yan ta’addan.

Rundunar soji ta karyata cewar yan Boko Haram sun kashe jami’anta

Rundunar soji ta karyata cewar yan Boko Haram sun kashe jami’anta

Kakakin sojojin ya bayyanawa majiyarmu ta Vanguard cewa a yanzu haka yana Maiduguri, jihar Borno.

KU KARANTA KUMA: Babu gwamnatin da tayi abunda Buhari yayi - Clark

Ya kuma roki yan Najeriya da su dana daukar ikirarin yan ta’addan da muhimmanci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel