Bayan kama matasa 20, wasu matasan sun cinnawa motar ‘yan sanda wuta a Legas

Bayan kama matasa 20, wasu matasan sun cinnawa motar ‘yan sanda wuta a Legas

Wannan shine karo na biyu da fusatattun matasa suka cinnawa motar jami’an ‘yan sanda wuta a yankin Ikorodu dake garin Legas.

Kazalika hukumar ta ‘yan sanda ta bayyana cewar ta kama a kalla mutane 20 da take zargin na da hannu a kone motar ‘yan sanda ta ofishin Layemi.

Wadanda aka kama din, yanzu haka, na can ofishin sahsen binciken laifukan ta’addanci na hukumar ‘yan sandan Legas dake kan titin Panti a unguwar Yaba.

Bayan kama matasa 20, wasu matasan sun cinnawa motar ‘yan sanda wuta a Legas

‘yan sanda

An kone motar ‘yan sandan ne a jiya bayan jami’an hukumar sun kai doki domin kwantar da rikicin da ya barke a tsakanin matasan unguwar Olumokun dake yankin Amukoko da na unguwar tititin Olayinka dukkan su a unguwar Ajegunle.

A yayin da matasan yankin Amukoko ke guduwa bayan jami’an ‘yan sanda sun tarwatsa su ne suka ci karo da motar ‘yan sandan ofishin Ajeromi kuma nan take suka cinna mata wuta kamar yadda Chika Oti, kakakin hukumar ‘yan sanda a jihar Legas ya sanar.

DUBA WANNAN: Handama da babakere: Majalisa ta tsige shugaban karamar hukuma a Kebbi

‘Yan sandan sun gaza hana matasan kone motar ne saboda kwamishinan hukumar a jihar Legas, Edal Imohimi, ya hana su amfani da bindiga wajen kwantar da tarzoma.

Kwamishina Imohimi ya umarci shugannin ofishin ‘yan sanda dake unguwar Ajegunle da kewaye da su tuntubi masu sarautar gargajiya na yankin domin yiwa tufkar rikici tsakanin matasan yankin hanci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel