Dalili guda da ya sanya 'yan sanda marin wasu jami’an VIO

Dalili guda da ya sanya 'yan sanda marin wasu jami’an VIO

- Jami'an 'yan sanda sun fusata don an karbi cin hanci a gaban idonsu

- Har ta kai ga sun kasa jurewa sun mammari jami'an da suka karbi cin hancin

- Sai da wasu suka shiga tsakani kafina a samu a sasanta

Jami’an kula da lafiyar ababen hawa (VIO) sun shassha mari da masga wurin ‘yan sanda a yau Litinin.

‘Yan sanda sunyi baranbarama, sun mammari wani jami’i

‘Yan sanda sunyi baranbarama, sun mammari wani jami’i

Jami’an ‘yan sandan da aka bayyana cewa suna cikin ayarin tawagar babban Sufeton ‘yan sanda na kasa, sun mammary jami’an ne bisa laifin karbar na goro a wurin masu tuka Babura (‘yan kabu-kabu).

Lamarin dai ya afku ne da misalign 11:20am na safe a yankin Ufuoma-Odovie dake karamar hukumar Ughelli ta jihar Delta. Kamar yadda wani da abin ya faru a idonsa ya shaidawa jaridar Vanguard.

KU KARANTA: Sojojin sama sunyi lugudan wuta a sansanin ‘yan bindiga a Zamfara

Tun farko dai ‘yan sanda dake a cikin rundunar X Squad suna tafiya ne cikin mota kirar Sienna mai shudin kala, kawai sai suka tsaya a daidai mararrabar da jami’an duba lafiyar ababen hawan suka kafa shingen bincike, suka hau da bugu bisa zarginsu da karbar cin hancin da ba’a bayyana ko nawa ne ba a wurin ‘yan Achaba

Shaidar gani da idon ya bayyana cewa ‘yan sandan sun zane su da mazugin wandonsu tare da dan sassama su sama-sama kafin daga bisani ragowar abokan aikinsu su shiga cikin maganar don rokon ayi musu afuwa.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel