Babu gwamnatin da tayi abunda Buhari yayi - Clark

Babu gwamnatin da tayi abunda Buhari yayi - Clark

Wani babban jigon Najeriya, Robert Clark yace babu wata gwamnati a Najeriya da tayi abunda shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi.

Clark ya bayyana hakan ne yayinda yake yabama yaki da rashawar gwamnatin Muhammadu Buhari.

Babban jigon wanda ya yi wannan furuci kwana daya bayan Shugaba Buhari ya sha alwashin tura wadanda suka sanya kasar a halin da tattalin arzikinta ke ciki gidan yari, ya lura cewa ya zama dole a bi tsarin doka.

Babu gwamnatin da tayi abunda Buhari yayi - Clark

Babu gwamnatin da tayi abunda Buhari yayi - Clark

Ya shawarci shugaban kasar a ya tabbatar da cewa yayi yaki kamar yadda kundin tsarin mulki ta tanadar ta hanyar kin sabama hakkin al’umma.

KU KARANTA KUMA: Hotunan yadda ake aikin Hajjin bana

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, 20 ga watan Agusta, yayi ganawar sirri tare da shuwagabannin tsaro a fadar shugaban kasa da ke Abuja, jaridar Nation ta rahoto.

A rahotanni da aka tattara, an gano cewa wannan ya kasance daya daga cikin ayyuka masu muhimmanci da shugaban kasar ya fara gudanarwa bayan dawowar shi Abuja daga hutun kwana 10 da yayi a birnin Landon.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel