APC ta lissafa zunuban Saraki 6 da suka zubar da mutuncinsa a idon ‘yan Najeriya

APC ta lissafa zunuban Saraki 6 da suka zubar da mutuncinsa a idon ‘yan Najeriya

A satin da ya gabata ne shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya sanar da wata jarida, Bloomberg, cewar yana tuntuba tare da bayyana cewar yana da niyya mai karfi ta yin takarar shugaban kasa.

A nata bangaren, jam’iyyar APC ta mayar da martini ga wannan buri na Saraki tare da kalubalantar sa cewar ba shi da kimar da ‘yan Najeriya zasu zabe shi a matsayin shugaban kasa saboda wasu zununai da ta lissafa kamar haka;

1. Badakalar almundahana da ta kai ga rushewar bankin Societe Generale Bank mallakar gidan su Bukola. Ana zargin Saraki da lalata fiye da N1bn na masu ajiya a bankin, lamarin da ya saka bankin durkushewa.

APC ta lissafa zunuban Saraki 6 da suka zubar da mutuncinsa a idon ‘yan Najeriya

Bukola Saraki

2. Facaka da kudin gwamnatin jihar Kwara, mayar da tukiyar gwamnatin jihar mallakar sad a wasu abokai lokacin da yake gwamna.

3. Tarihin iya cin amana, kassara: ‘yan uwa da jam’iyyun siyasa (APC da PDP), majalisar dattijai da ma gwamnatin tarayya.

Sashen binciken laifukan damfara na tuhumar Saraki da badakalar kudi, N11bn, a tsohon bankin Intercontinental.

DUBA WANNAN: Allah ya yiwa daya cikin jaruman fina-finan Hausa rasuwa

4. Mallakar kadarori masu tsada da boye wasu kadarorin nmasu dumbin a kasashen dake fadin duniya kamar yadda jaridar Turai, Panama, ta bankado.

5. Kirkiro dokokin bogi a majalisar dattijai domin samun dammar zama shugabanta da kuma jagorantar aringizon kudade a kasafin kudin kasa.

6. Kirkirar wani tsarin aikin noma na bogi mai taken “Shonga” na miliyoyin daloli lokacin da yake gwamna da kuma hannunsa a badakalar $19.5bn na faris kulob.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel