Ina da kwarjinin da zan iya karawa da Buhari – Tambuwal ya maida martani ga Tinubu

Ina da kwarjinin da zan iya karawa da Buhari – Tambuwal ya maida martani ga Tinubu

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, yace da ace ya so hakan da yayi takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) domin yana da karjinin da zai iya karawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 20 ga watan Agusta yayinda yake maida martani ga jawabin shugaban APC, Ahmed Tinubu, game da barinsa jam’iyya mai mulki.

Gwamnan ya wallafa hakan ne a shafin @sokotogovthouse na twitter.

Ina da kwarjinin da zan iya karawa da Buhari – Tambuwal ya maida martani ga Tinubu

Ina da kwarjinin da zan iya karawa da Buhari – Tambuwal ya maida martani ga Tinubu

A baya mun ji cewa babban Jigon APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yayi kaca-kaca da wadanda su ka bar Jam’iyyar APC mai mulki inda yace gigin shugabancin kasar nan ke damun su kuma a-dawo-lafiya.

KU KARANTA KUMA: Hotunan yadda ake aikin Hajjin bana

Tinubu da yake jawabi a Legas yace irin su Bukola Saraki da Aminu Tambuwal sun fice daga APC ne domin sun san ba za su kai labari ba a Jihohin su idan su ka cigaba da zama a Jam’iyyar mai mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel