Sauya shekar jam'iya: Shure shure bazai hana mutuwa ba -Archbishop Okoh

Sauya shekar jam'iya: Shure shure bazai hana mutuwa ba -Archbishop Okoh

- Sauyin shekar jam'iya ba zai taba haifarwa kasar nan d'a mai ido ba.

- Rashin godiyar Allah ke haifar da matsaloli da yawa

- A baya bayan nan dai 'yan siyasa da dama sun sauya sheka daga jam'iyar da suke ciki zuwa wata jam'iyar, lamarin da ya jawo cece-kuce a kasar.

Sauya shekar jam'iya: Shure shure bazai hana mutuwa ba -Archbishop Okoh

Sauya shekar jam'iya: Shure shure bazai hana mutuwa ba -Archbishop Okoh

Wani babban malamin addinin kirista, Archbishop Nicholas Okoh ya shaidawa 'yan siyasar Nigeria cewa tsalle tsallen sauya sheka daga jam'iya zuwa wata jam'iyar ba zai taba magance matsalolin da kasar ke fuskanta ba.

Archbishop Okoh ya bayyana haka ne a majami'ar "All Saints Cathedral" dake garin Onitsha, jihar Anambra, a yayin taron wa'azi da bikin murnar zagayowar ranar haihuwar matar takwaran sa na jihar Niger, Dr. Mrs. Elsie Nwokolo.

KU KARANTA WANNAN: An yi batakashi tsakanin rundunar soji da makiyaya a Benue

Malamin addinin Kiristan, wanda ya samu wakilcin matarsa Mrs Nkasiobi Okoh da Bishop David Onuoha, ya bukaci 'yan siyasa da su kasance masu aiwatar da ayyukan raya kasa ga jama'ar da suka zabe su, tare da godewa Allah akan ni'imomin da yayi masu maimakon sauye sauyen jam'iyyu.

A cewar sa: "Idan ya zamana cewa baka godiyar Allah, zaka ci gaba da fuskantar matsaloli, amma idan kana gode masa akan ni'imomin da yayi maka, to kullum zai ci gaba da magance maka matsalolinka.

"Sauyin shekar jam'iya ba zai kai 'yan siyasa da kasar nan tudun mun tsira ba, domin kuwa shure shure ba ya hana mutuwa, mafita kawai itace yin ayyukan da zasu bunkasa rayuwar jama'a da kuma yiwa Allah godiya akan ni'imominsa"

Domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel