Yan ta’adda sun hallaka akalla mutane 19 a sabon harin Borno

Yan ta’adda sun hallaka akalla mutane 19 a sabon harin Borno

Akalla mutane 19 ne suka mutu a harin da yan ta’addan Boko Haram suka kai wani kauye a arewa maso gabashin Najeriya a safiyar ranar Lahadi, 19 ga watan Agusta, inji wani da ya tsira daga harin.

Wannan shine sabon hari da yan ta’addan Boko Haram suka kai yankin.

Yan ta’addan sun kai hari ne a kauyen Mailari dake yankin Guzamala na jihar Borno da misalign karfe 2:00 na dare, a cewar wani da ya tsira daga harin, Abatcha Umar.

Umar yace ya kirga mtane 19 da aka kashe, ciki hadda kaninsa. Wani bai bayar da agaji ga wadanda suka tsira a sansanin, sannan ya nemi a sakaya sunasa yace mutanen da suka mutu sun kai 63.

Yan ta’adda sun hallaka akalla mutane 19 a sabon harin Borno

Yan ta’adda sun hallaka akalla mutane 19 a sabon harin Borno

Ya kara da cewa an gano yan ta’addan a kauyen kimanin kwanaki uku kafin harin, ya kara da cewa mazauna yankin sun gargadi sojojin Najeriya dake kusa da garin Gudumbali amma babu wani mataki da aka dauka.

KU KARANTA KUMA: Ba Saraki ne ya haddasa gazawarku ba – Sanatoci ga APC

Ma’aikaci agajin yace daruruwan mutane daga kauyuka a yankin sun gudu zuwa sansanin yan gudun hijira da yake aiki a Munguno.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel