Laifin majalisa ne zalla kin amincewa da kasafin kudin hukumar zabe – Fadar shugaban kasa

Laifin majalisa ne zalla kin amincewa da kasafin kudin hukumar zabe – Fadar shugaban kasa

- Barin majalisa da na zartarwa na zargin juna kan jan kafa wurin sahalewa kasafin kudin hukumar zabe

- Tun farko dai majalisar kasar nan ce ta bayyana yadda fadar shugaban kasa suka haddasa tsaikon, amma a jiya fadar shugaban kasar suka mayar da martani

Fadar Shugaban kasa ta mayar da martani akan zargin da shugaban majalisar dattawa Dr. Abubakar Bukola Saraki yayi na cewa shugaba Muhammadu Buhari ne ya ke jan kafa akan amincewa da karin kasafin kudi na hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa wato (INEC).

Laifin majalisa ne zalla kin amincewa da kasafin kudin hukumar zabe – Fadar shugaban kasa

Laifin majalisa ne zalla kin amincewa da kasafin kudin hukumar zabe – Fadar shugaban kasa

Jawabin hakan ya fito ne daga bakin Malam Garba Shehu, babban mataimaki ga shugaban kan harkokin watsa labarai, wanda ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a Abuja jiya Lahadi.

KU KARANTA: Koda PDP ce ta samu nasara a 2019 zamu yarda – Osinbajo

Garba shehu ya ce "Saraki yana da wani kuduri da ya dauki azamar cimmawa domin kawo tangarda wajen shirye-shiryen zaben da ake yi".

“Ba gaskiya batun cewa wai hukumar ta gabatar da kasafin kudin ga fadar shugaban kasa tun a watan Fabarairu, wannan babu gaskiya a cikin maganar".

“Maganar gaskiya ita ce an gabatar da kasafin kudin bayan da shugaban kasa ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2018, wanda hakan ya zama cikon gibin kasafin kudin ke nan"

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel