Gwamna Nyesom Wike ya koka game da zaben Jihar Ribas ya zargi APC da hada-kai da 'Yan Sanda

Gwamna Nyesom Wike ya koka game da zaben Jihar Ribas ya zargi APC da hada-kai da 'Yan Sanda

Mun samu labari cewa Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike, ya koka game da abin da ya faru a zaben da aka yi a Jihar sa kwanan nan inda yace Jami’an tsaro su na shiga cikin lamarin zabe domin kawo rudani.

Gwamna Nyesom Wike ya koka game da zaben Jihar Ribas ya zargi APC da hada-kai da 'Yan Sanda

Nyesom Wike yace 'Yan Sanda na yi wa APC aiki a Jihar Ribas

Gwamna Wike yayi jawabi a kafofin yada labaran Jihar Ribas a karshen makon nan inda yayi tir da dage zaben Majalisar dokokin wani Yanki da ake gabtarwa da Hukumar INEC ta yi. Gwamnan yace ana neman mutanen sa da rigima.

Nyesom Wike ya zargi Gwamnatin Tarayya da kuma Jam’iyyar APC mai mulki da amfani da Jami’an tsaro na ‘Yan Sanda wajen yunkurin murde zaben Garin Fatakwal. Gwamnan yace ‘Yan Sanda ne su ka kawo hargitsi har aka tsaida zaben.

KU KARANTA: Babban Jigon APC Tinubu yace Wike ya sa Tambuwal ya bar APC

Gwamnan ya nuna cewa ba yau Jami’an tsaro su ka fara yi wa zabe katsalandan a Jihar ba don haka yace ana neman bacin ran mutanen Jihar Ribas. Wike yace babu wanda zai tursasawa mutanen Jihar ta sa abin da ba sa so a kasar nan.

Nyesom Wike yace duk da tabbacin da Kwamishin ‘Yan Sandan Jihar ya bada na cewa za ayi gaskiya a zaben da ya gabata, hakan bai tabbata ba. Wike ya kuma ce ‘Yan Sanda sun hada kai ne da APC wajen tada kura zaben maimakon samar da tsaro.

Shi ma dai tsohon Shugaban PDP Ahmed Makarfi ya gargadi Gwamnatin Tarayya ta shafawa Jihar Ribas lafiya ta daina muzgunawa PDP da sunan siyasa. Manyan na PDP sun zargi APC da amfani da Jami’an tsaro wajen tada rikici a zaben da ya gabata

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel