Hukumar Kwastam ta gano wata sabuwar almundahanar da akewa Shinkafa a kasar nan

Hukumar Kwastam ta gano wata sabuwar almundahanar da akewa Shinkafa a kasar nan

- Jami'an hana hana fasa kwauri ta kasa sun ce an yi walkiya

- Sun gano yadda 'yan kasuwa ke sayar da Shinkafa 'yan gida a matsayin 'yar waje

Hukumar hana fasa kwauri ta kasa ta bankado wata almundahanar da ‘yan kasuwa suke yi akan Shinkifar cikin gida wajen nunawa masu saya a matsayin Shinkafa yar waje.

Wannan na zuwa ne cikin jawabin da sabon babban jami'in Kwastam mai lura da sashen bincike dake Ikeja Mohammed Aliyu yayi a lokacin da yake karbar aiki daga gurin Muhammad Uba cikin karshen makon da ya gaba ta.

Hukumar Kwastam ta gano wata sabuwar almundahanar da akewa Shinkafa a kasar nan

Hukumar Kwastam ta gano wata sabuwar almundahanar da akewa Shinkafa a kasar nan

Mohammed Aliyu ya kara da cewa hukumar ta Kwastam ta samu nasarar damke buhunan da aka haramta amfani da su masu nauyin 738 a ma'aunin Kiligiram, wanda kudinsu ya kai sama da Naira miliyan 175.

Sannan sun kuma kama wata Shinkafa buhu 190 da aka zuba a cikin jarkoki, wanda kudinta ya kai kimanin Naira miliyan N178m.

KU KARANTA: Chabdi jan: ‘Yan sanda sun yiwa wani Ango kamun kazar kuku ranar aurensa

Sabon shugaban ya kuma yi alkawarin zai dora daga inda wanda ya karbi aiki daga hannunusa, musamman dakile harkar fasakwauri.

Sannan ya bayyana cewa “Da yawa daga cikin shinkafar da kuke gani a kasuwa, shinkafa ce wacce aka noma ta a gida, amma da yake al'ummar kasar nan sun fi son shinkafar waje, hakan ya sanya ake saka mata buhu irin na Shinkafa ‘yar waje domin jan hankalin ‘yan kasar nan".

“Mafi yancin Shinkafar ana sarrafata ne a karamar hukumar Kura dake jihar Kano, amma kuma sai a sanya mata buhuna masu tambarin waje. Sai dai abu mafi muhimmanci shi ne yin la'akari da abinda yake ciki ba wai abin da yake wajen ba".

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel