APC ce ta kore ni ba ni na bar ta ba Inji tsohon Mataimakin Ganduje da ke tare da Kwankwaso

APC ce ta kore ni ba ni na bar ta ba Inji tsohon Mataimakin Ganduje da ke tare da Kwankwaso

Kun san cewa Farfesa Hafiz Abubakar ya bar mukamin sa na Mataimakin Gwamnan Jihar Kano kwanaki inda ya koka da banbancin akida da kuma muzguna masa da Gwamnatin Ganduje ta ke yi tun a karshen shekarar bara.

APC ce ta kore ni ba ni na bar ta ba Inji tsohon Mataimakin Ganduje da ke tare da Kwankwaso

Hafiz Abubakar ya bar APC ya koma Jam'iyyar PDP

Dama tun a shekarar bara Mataimakin Gwamnan ya bayyana cewa ba zai yi takara da Gwamna Ganduje a 2019 ba. Farfesa Abubakar yace zai koma Jami’a ne inda ya fi wayau ya cigaba da koyarwa domin zama fa a APC ba ta sa bace.

Kwanan nan dai Hafiz Abubakar din ya koma Jam’iyyar PDP inda ya bi tsohon Mai gidan sa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Farfesan yayi hira da Jaridar Daily Trust inda yace siyasa ba za ta hana sa karantarwa a Jami’a ba.

KU KARANTA: Ganduje yace idan Kwankwaso ya haifu ya shigo Kano

Tsohon Mataimakin Gwamnan yake cewa irin su Marigayi Malam Aminu Kano su na da ‘Dalibai duk da su na cikin siyasa tsamo-tsamo. Yanzu haka Farfesa Abubakar yace akwai manyan ‘Daliban da yake da duba aikin su a Jami’a.

Hafiz Abubakar yace tun a 1998 su ke tare da Abdullahi Ganduje kuma sun yi aiki tare ya fi a kirga. Abubakar yace kawo yanzu bai yi da-na-sanin sa shiga siyasa ba inda yace dama ya saba kiran mutanen kirki su shiga harkar.

Sai dai abin da ba a sani ba shi ne ko tsohon Mataimakin Gwamnan zai yi takara a zaben 2019. Wasu dai na ganin watakila ya marawa ‘Dan takarar Jam’iyyar PDP Salihu Sagir Takai baya a tika Ganduje da kasa a zabe mai zuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel