An yi batakashi tsakanin rundunar soji da makiyaya a Benue

An yi batakashi tsakanin rundunar soji da makiyaya a Benue

Kwamandan rundunar atisayen soji ta "Operation Whirl Stroke", Manjo Janar Adeyemi Yekini, ya tabbatar da cewa rundunar soji sunyi batakashi da makiyaya a karamar hukumar Guma dake jihar Benue, a ranar asabar.

Karamar hukumar Guma dai ta dade tana fuskantar hare-hare daga mutanen da ake kyautata zaton makiyaya ne, tun daga watan Janairu na wannan shekarar, wanda yayi sanadiyar rasa rayukan sama mutane 500.

KU KARANTA WANNAN: Jonathan bai ceto 'yan matan Chibok ba - BBOG

Kwamandan ya ce babu rauni kon asarar rayuka a bangarorin biyu.

Yace: "Rundunar sojinmu sun fita rangadi a yankin Gbajimba inda suka ci karo da wasu makiyaya, sun yi musayar wyta, sai dai ba'a samu asarar rayuka ko rauni ba, duk da cewa har yanzu sojojin na a filin dagar. Duk da haka, zan ci gaba da sanar daku abunda ke faruwa"

Sakamakon rahotan da wakilinmu ya hada mana, ya nuna cewa tun a safiyar ranar asabar ne wasu da ake zargin makiyaya ne sun farwa wata tawagar soji dake rangadi a karamar hukumar Guma, inda suka kashe soja daya tare da jikkata wasu biyu.

Rahotannin sun bayyana cewa lamarin ya afku ne a safiyar ranar, yayinnda sojojin ke rangadi kan hanyar Gbajimba zuwa Iyordye zuwa Akaahena, inda ba zato makiyayan suka far masu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel