Idan ka isa: Gwamna Ganduje ya kalubalanci Sanata Kwankwaso game da wani muhimmin lamari

Idan ka isa: Gwamna Ganduje ya kalubalanci Sanata Kwankwaso game da wani muhimmin lamari

Siyasar jihar Kano ta cigaba da dumama biyo bayan kalubalantar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje yayi a ranar Lahadi, 19 ga watan Agusta, inda yace idan ya isa ya shiga Kano ya kaddamar da takarar shugaban kasa, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Ganduje ya bayyana haka ne a yayin bikin tallafa ma mata 6,600 da jarin naira dubu ahsirin ashirin, inda yace Kanawa ba zasu taba yin maraba da shigowar Kwankwaso jihar Kano ba.

KU KARANTA: APC ta sayi kuri'u don cin zaben sanatan Katsina ta Arewa acewar Kaita

Idan ka isa: Gwamna Ganduje a kalubalanci Sanata Kwankwaso game da wani muhimmin lamari

Kwankwaso Ganduje

“Kanawa nada ikon yin fatali da shi, kai tuni ma munyi fatali da shi, bamu taba kallonsa a matsayin wani muhimmin dan takarar shugaban kasa ba, kuma mu bamu san kowa ba sai shugaban kasa Muhammadu Buhari, shi kansa Kwankwaso ya san Kanawa zasu yi amfani da kuri’unsu wajen shafe babinsa a siyasance.” Inji Ganduje.

Gwamnan ya bayyana ma mahalarta taron cewa duk gobarar da kasuwannin jihar Kano suka yi, Kwankwaso bait aba zuwa don ya jajanta musu ba, ballantana ya tallafa musu, alhali duk masu kishin jihar Kano sun bada nasu taimako, inji shi.

Da yake tsokaci game da tallafin da gwamnatin jihar Kano ta baiwa Matan, Gwamna Abdullahi Ganduje yace sun yi haka ne don inganta rayuwar jama’a, tare da rage musu radadin talauci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel