Yanzu-Yanzu: Hadiman Gwamna Tambuwal 252 sun yi murabus daga gwamnatin sa

Yanzu-Yanzu: Hadiman Gwamna Tambuwal 252 sun yi murabus daga gwamnatin sa

Akkala ba akasara ba mutane dari biyu da hamsin da biyu ne dai dake zaman hadiman Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal sukayi murabus daga mukaman su da ya nada su.

Wadanda suka ajiye mukaman nasu sun bayyana cewa sun yanke shawarar daukar wannan matakin ne na murabus saboda canza shekar da gwamnan yayi daga jam'iyyar su ta All Progressives Congress (APC) zuwa jam'iyyar PDP a 'yan kwanakin nan da suka gabata.

Yanzu-Yanzu: Hadiman Gwamna Tambuwal 252 sun yi murabus daga gwamnatin sa

Yanzu-Yanzu: Hadiman Gwamna Tambuwal 252 sun yi murabus daga gwamnatin sa

KU KARANTA: An bayyana adadin yan majalisun da za su iya tsige Saraki

Legit.ng ta tuna cewa a kwanan baya dai gwamnan jihar kuma tsohon kakakin majalisar wakillai a tarayyar Najeriya ya sanar da ficewar sa daga jam'iyyar APC zuwa PDP.

A wani labarin ma dai, Gwamnan jihar Benue dake a arewacin Najeriya ya bayyana cewa tun da ya fice daga APC ya koma PDP yake ta fuskantar matsalolin rayuwa da kunci sakamakon irin yadda hukumomin gwamnatin tarayya ke yi masa bita-da-kulli,

Gwamna Samuel Ortom na Benue din ya bayyana hakan ne a lokacin da yake fira da wakilin majiyar mu na Vanguard lokacin da yake ansa tambayoyi daga gare shi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel