Yadda gwamna Abiola Ajimobi yayi Amai ya lashe bayan shekaru 2

Yadda gwamna Abiola Ajimobi yayi Amai ya lashe bayan shekaru 2

- Magana zarar bunu in ji masu iya magana

- Bayan shekaru biyu da tabbatar da cewa ba zai rusa wani gini ba, karshe ya ruguza sa

- Duk da har kawo yanzu gwamnatin jihar bata ce komai ba, amma ana kyautata zaton ruguza shin na da alaka da siyasa

Kimanin shekaru biyu kenan da yin furucin da gwamnan jihar Oyo Abiola Ajimobi ya yi akan cewa babu dalilin da zai sa ya rushe gidan shahararren mawakin nan Yinka Ayefele da ke birnin Oyo.

Yadda gwamna Abiola Ajimobi yayi Amai ya lashe bayan shekaru 2

Yadda gwamna Abiola Ajimobi yayi Amai ya lashe bayan shekaru 2

Cikin wata zantawa da gidan radiyon jihar ta Oyo yayi da shi, wanda Premium Times suka samu dauke da muryar gwamna Ajimobi yana furucin ba yadda za’ai ya rushe gidan, mamakin Jim kadan da rantsar da shi a matsayin gwamanan jihar ta Oyo.

Wasu rahotanni da jaridar ta rawaito sun nuna cewa a safiyar Lahadin ya aka wayi gari da fara rushe gidan Ayefelen , wanda gidan radiyon Fresh FM yake hade da ginin.

Tun da farko dai a cikin shekarar 2016 an tambayi Ajimobi akan ko zai rushe ginin gidan Radiyon Fresh FM a zangon mulkinsa na farko, saboda yadda gidan radiyon suke yawaita adawa da shi.

Sai ya kada ba ki ya ce “Lokacin da muka yi takarar zaben gwamna a karon farko, bayan mun yi nasara mutane da yawa sun yi kira akan mu rushe gidan Fresh FM, saboda yadda ya dinga adawa tare da saka wasu wakoki da ake zaginmu"

KU KARANTA: Maganar ta fito: Da kyar da jibin goshi aka cire Lawal Daura daga mukaminsa

“Ban ga dalilin da zai sanya in rushe gidan Radiyon ba, Idan Ayefele baya goyon bayanmu a yanzu, to nan gaba zai zama daga cikin masu goya mana baya. Ayefele yana tare da ni, kuma ina fatan bunkasar kasuwancinsa".

Ya kara da cewa" Gidan Radiyon Fresh FM yafi kowanne gidan Radiyo inganci da kyau a fadin jihar Oyo".

Yadda gwamna Abiola Ajimobi yayi Amai ya lashe bayan shekaru 2

Yadda gwamna Abiola Ajimobi yayi Amai ya lashe bayan shekaru 2

Amma sai dai duk da irin wannan maganganu na gwamna Ajimobi sai ga shi yau da safe an wayi da fara rushe ginin tashar Radiyon, bisa dalilin sabawa hukumar kula da tsara birane ta jihar Oyo tare kuma da zargin da gwamnatin jihar ta yi akan ginin ya saba da dokar kula da tsara birane ta jihar Oyo.

Kwamishinan yada labarai na jihar Toye Arulogun, ya bayyana cewa gwamnati ta karbi korafin mutanen akan hadduran ababen hawa har 3 da suka faru a yankin ginin.

Da yake mayar da martani akan aikin rushe ginin nasa, Ayefele ya rubuta a shafinsa na sada zumunta na Facebook cewa gwamnatin jihar ta kaddamar da kudiranta.

“A karshe dai Jihar Oyo ta aikata.... Cikin takaici da Jimami, Allah ka kawomin gudummawa".

Kawo yanzu dai babu wata sanarwa daga gwamnatin jihar ta Oyo akan rushe ginin gidan Radiyon wanda ake kiyasin darajarsa ta kai kimanin Naira miliyan N800m.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel