Gwamnan Taraba yayi karin haske game da jifar Sanatan Buhari da matasa suka yi

Gwamnan Taraba yayi karin haske game da jifar Sanatan Buhari da matasa suka yi

Gwamnan jihar Taraba dake a Arewa maso gabashin Najeriya Mista Tarius Ishaku a ranar Lahadi yayi karin haske game da jifar ministar mata da cigaban al'umma a gwamnatin shugaba Buhari Sanata Aisha Alhassn da wasu matasa sukayi a ranar Asabar din da ta gabata.

Ministar dai wadda matasan suka yiwa ruwan duwatsu a karamar hukumar Takum ta jihar Taraba ta je ne domin duba yadda zaben cike gurbin da aka yi na dan majalisar jihar ta zargin gwamnatin jihar ne da dauko hayar matasan.

Gwamnan Taraba yayi karin haske game da jifar Sanatan Buhari da matasa suka yi

Gwamnan Taraba yayi karin haske game da jifar Sanatan Buhari da matasa suka yi

KU KARANTA: Gwamnoni 9 da za suyi bikin sallah na karshe a mulki

Legit.ng ta samu cewa sai dai a martanin da gwamnan ya mayar ta bakin mai taimaka masa na musamman akan harkokin yada labarai, Mista Bala Dan-Abu ya wanke kansa inda yace shi ma sai dai ya ji a labarai cewar an jefe ta din amma bai da masaniya.

A wani labarin kuma,Gwamnan jihar Benue dake a arewacin Najeriya ya bayyana cewa tun da ya fice daga APC ya koma PDP yake ta fuskantar matsalolin rayuwa da kunci sakamakon irin yadda hukumomin gwamnatin tarayya ke yi masa bita-da-kulli,

Gwamna Samuel Ortom na Benue din ya bayyana hakan ne a lokacin da yake fira da wakilin majiyar mu na Vanguard lokacin da yake ansa tambayoyi daga gare shi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel