Rikita-rikita: APC na shirin rasa wani gwamnan zuwa PDP

Rikita-rikita: APC na shirin rasa wani gwamnan zuwa PDP

- Guguwar sauyin sheka na cigaba da kadawa Gabas da Yamma, Kudu da Arewa

- Bayana rasa gwamnoni zuwa jam'iyyar adawa, APC na daf da sake rasa wani gwamnan nata a cewar wata majiya

Jirgin sauyin shekar 'yan siyasa a Najeriya na cigaba da shawagi domin dibar wadanda suke da burin canza gidan kafin zaben 2019, inda ake hasashen da yiwuwar gwamnan jihar Adamawa Jibrilla Bindow zai iya ficewa daga jam'iyyar APC.

Jaridar Punch a yau lahadi ta rawaito cewa gwamnan ya fara tattaunawa da jam'iyyar PDP domin ganin ya cimma matsaya wajen komawarsa cikinta.

Rikita-rikita: APC na shirin rasa wani gwamnan zuwa PDP

Rikita-rikita: APC na shirin rasa wani gwamnan zuwa PDP

Duk da cewa gwamnan a kwanakin baya ya musanta zargin da ake na cewa zai iya ficewa daga jam'iyyar ta APC, amma wakilin jaridar Punch ya rawaito cewa bayanai masu karfi sun nuna gwamnan zai iya ficewa daga jam'iyyar.

Kamar yadda wata majiya ta rawaito, gwamnan ya gindaya wasu sharuda kafin ya koma tsohuwar jam'iyyar tasa.

Ita ma jam'iyyar ta PDP ta rawaito cewa dukkanin wanda suka fice daga jam'iyyar tare da gwamnan a shekara ta 2014 suna sa ran zasu dawo kafin babban zabe na 2019.

KU KARANTA: Koda PDP ce ta samu nasara a 2019 zamu yarda – Osinbajo

Da majiyar ta tuntubi sakataren jam'iyyar PDP reshen jihar ta Adamawa Abdullahi Prambe, ya ce suna cigaba da yin duk mai yiwuwa don ganin sun shawo kan Bindow ya komo cikinsu.

Mai baiwa gwamnan shawara akan harkokin yada labarai Macaulay Hunohashi, ya ce gwamnan "Har yanzu da ne ga jam'iyyar ta APC kuma baya tunanin ficewa daga cikinta".

Ya kara da cewa "Bindow ba shi da tunanin ficewa daga jam'iyyar APC, yana nan a cikinta kuma zai cigaba da marawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari baya don ganin ya lashe zaben 2019".

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel