Tunda na bar APC ni ke ta fuskantar matsaloli - Inji wani gwamnan Arewa

Tunda na bar APC ni ke ta fuskantar matsaloli - Inji wani gwamnan Arewa

Gwamnan jihar Benue dake a arewacin Najeriya ya bayyana cewa tun da ya fice daga APC ya koma PDP yake ta fuskantar matsalolin rayuwa da kunci sakamakon irin yadda hukumomin gwamnatin tarayya ke yi masa bita-da-kulli.

Gwamna Samuel Ortom na Benue din ya bayyana hakan ne a lokacin da yake fira da wakilin majiyar mu na Vanguard lokacin da yake ansa tambayoyi daga gare shi.

Tunda na bar APC ni ke ta fuskantar matsaloli - Inji wani gwamnan Arewa

Tunda na bar APC ni ke ta fuskantar matsaloli - Inji wani gwamnan Arewa

KU KARANTA: Yadda wasu masoya suka kwashi 'yan kallo a Kano

Legit.ng ta samu cewa Gwamna Ortom ya ce yanzu dai duk da a iya cewa siyasa ce, amma irin yadda hukumomin tsaron kasar ke bibiyar sa da kuma al'ummar jihar sa babban abun takaici ne da ya kamata kowa yayi tir da shi.

A wani labarin kuma, Daya daga cikin yan takarar shugaban kasa a Najeriya dake da kudurin tunkarar Shugaba Buhari a zabe mai zuwa kuma shugaban gidan Jaridar nan ta Sahara Reporters ya yi alkawarin mai da mafi karancin albashin ma'aikata zuwa Naira dubu dari idan har ya zama shugaban kasa a 2019.

Dan takarar mai suna Omoyele Sowore da ya fito daga yankin yarbawan Najeriya ya bayyana hakan ne a garin Abuja yayim da yake zantawa da yan jarida a dakin taro na unguwar Lugbe, babban birnin tarayya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel