Wani dan takara yayi alkawarin maida albashi mfi karanci Naira dubu 100 in ya zama shugaban kasa

Wani dan takara yayi alkawarin maida albashi mfi karanci Naira dubu 100 in ya zama shugaban kasa

Daya daga cikin yan takarar shugaban kasa a Najeriya dake da kudurin tunkarar Shugaba Buhari a zabe mai zuwa kuma shugaban gidan Jaridar nan ta Sahara Reporters ya yi alkawarin mai da mafi karancin albashin ma'aikata zuwa Naira dubu dari idan har ya zama shugaban kasa a 2019.

Dan takarar mai suna Omoyele Sowore da ya fito daga yankin yarbawan Najeriya ya bayyana hakan ne a garin Abuja yayim da yake zantawa da yan jarida a dakin taro na unguwar Lugbe, babban birnin tarayya.

Wani dan takara yayi alkawarin maida albashi mfi karanci Naira dubu 100 in ya zama shugaban kasa

Wani dan takara yayi alkawarin maida albashi mfi karanci Naira dubu 100 in ya zama shugaban kasa

KU KARANTA: Manyan mata sun yi zanga-zanga a tsirara a jihar Imo

Legit.ng ta samu cewa haka kuma matashin ya bayyana African Action Congress (AAC) a matsayin jam'iyyar da zai yi takarar shugabancin kasar a karkashin inuwar ta.

A wani labarin kuma, Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau Independent National Electoral Commission (INEC) ta bayyana cewa batada wani kudiri na boye ko na zahiri na daga zaben gama gari da ta shirya gudanarwa a shekarar 2019.

Shugaban hukumar ta Independent National Electoral Commission (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu shine ya sanar da hakan a lokacin da yake ansa tambayoyi daga 'yan kwamitin majalisar wakilai a ranar Juma'ar da ta gabata.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel