Shugaba Buhari ya rubuwata majalisa wasika

Shugaba Buhari ya rubuwata majalisa wasika

- Bayan daukar hutun aiki na tsawon kwanaki 10, shugaba Buhari ya dawo aiki

-Yanzu haka ya aike wasikar karbar aiki a hukumance daga hannun mataimakinsa

- Shugaban na fuskantar suka mai tsanani daga mutane sakamakon yawan tafiye-tafiye zuwa kasashen ketare

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikewa da majalisar kasa takardar shaidar dawowarsa bakin aiki a matsayinsa na shugaban kasar tarayyar Najeriya.

Shugaba Buhari ya rubuwata majalisa wasika

Shugaba Buhari ya rubuwata majalisa wasika

Hakan ya fito ne daga bakin mai baiwa shugaban kasa shawara akan harkokin yada labarai malam Garba Shehu, a jiya asabar a babban birnin tarayya.

KU KARANTA: Koda PDP ce ta samu nasara a 2019 zamu yarda – Osinbajo

Mai baiwa shugaban kasar shawarar yace wasikar an aike ta ne zuwa ga majalisun domin shaida musu kawo karshen hutun da shugaba Buhari ya dauka na tsawon kwanaki goma.

A cikin wasikar wadda aka yi wa taken “Dawowa bakin aiki” wadda take dauke da sa hannun shugaban kasar, ya ce "Bisa dokar sashi na 145 karkashin kundin tsarin mulki na shekara ta 1999, ina mai rubutawa majalisar wakilai cewa na dawo bakin aiki bayan hutun kwanaki goma da na dauka".

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel