Gudun tsigewa: Saraki da Dogara zasu gudanar da zaman majalisa na hadin gwuiwa

Gudun tsigewa: Saraki da Dogara zasu gudanar da zaman majalisa na hadin gwuiwa

Wani rahoto da jaridar PUNCH ta wallafa na ranar Lahadi ya bayyana wasu mambobin majalisar dattijai dake biyayya ga shugaban majilasar dattijai, Bukola Saraki, suka bullo da wata dabara domin hana tsige shi da mataimakinsa daga mukaminsu ba.

Jaridar ta bayyana cewar bayan saka idanu a kan mambobin majalisar daga jam’iyyar APC, masu biyayya ga Saraki sun gama kamala duk wani shirin domin ganin Saraki ya cigaba da zama shugaban majalisar har bayan ranar 25 ga watan Satumba.

Wani binciken jaridar ya tabbatar da cewar Saraki ya tuntubi Dogara a waccan asabar din domin janye batun dawowa daga hutun da majalisar ta tafi a cikin satin da ya gabata.

Gudun tsigewa: Saraki da Dogara zasu gudanar da zaman majalisa na hadin gwuiwa

Saraki da Dogara
Source: Depositphotos

Canja shawarar dawowar majalisar daga hutun ya biyo bayan tafiya aikin Hajji da wasu ‘yan majalisa dake goyon bayan Saraki suka yi kamar yadda wasu sanatoci da basu yarda a ambaci sunansu ba suka sanar da jaridar ta Punch.

Majalisar na son dawowa daga hutun da ta tafi ne bayan fadar shugaban kasa ta bukaci su amince da kasafin kudin da hukumar zabe mai zaman kanta zata yi amfani da su domin gudanar da zabukan 2019.

Sai dai sabanin dawowar majalisar kamar yadda tayi alkawari, sai mambobin hadin gwuiwar majalisar ne suka zauna da hukumar INEC domin tattauna batun kasafin kudin.

DUBA WANNAN: Osinbajo ya saka hannu a kan wasu muhimman dokoki 3

Wata dabara da mambobin majalisar masu son ganin ba a tsige Saraki ba suka bullo da ita, it ace ta batun yin zaman hadin gwuiwa domin zartar da kasafin kudin hukumar ta INEC.

Wani Sanata daga yankin arewa maso yamma ya bayyana cewar hakan zai tabbatar da cewar ba a tayar da maganar tsige Saraki ba tunda doka bata yarda a tattauna irin wadannan maganganun ba yayin zaman hadin gwuiwar majalisa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel