Dalilin da ya sanya muke so Buhari ya ci gaba har bayan 2019 - Gwamna Bello

Dalilin da ya sanya muke so Buhari ya ci gaba har bayan 2019 - Gwamna Bello

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana babba dalilin da ya sanya al'ummar kasar na masu kishi ke muradin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zarce har bayan 2019.

Gwamnan yake cewa, shawarar da masu kishin kasar nan su yanke na goyon bayan shugaba Buhari har bayan 2019 ba wani abu face tsagwaran neman hakikanin jagoranci na gaskiya gami da adalci.

Gwamna Bello ya bayyana hakan ne yayin amsa tambayoyin manema labarai na kasa da kasa, inda ya ce shugaba Buhari ya ceto tattalin arzikin kasar nan daga zagwanyewa duba da irin ibtila'in da gwamnatin bayan ta jefa shi a ciki.

A mahangar gwamna Bello, 'yan Najeriya na ci gaba da kasancewa cikin farin ciki karkashin gwamnatin shugaba Buhari gami da gamsuwa da nagarta irin ta gaskiya da rikon amanar sa.

Dalilin da ya sanya muke so Buhari ya ci gaba har bayan 2019 - Gwamna Bello

Dalilin da ya sanya muke so Buhari ya ci gaba har bayan 2019 - Gwamna Bello

Ya ke cewa, abin takaici ne a kullum ba bu abinda 'yan adawa suka nufata sai ganin bayan gwamnatin sa domin cimma manufar su ta karbar ragamar mulki da za su ci gaba da bushasha iyakacin son ran su.

KARANTA KUMA: Gwamna Ganduje ya sallami Fursunoni 170 a jihar Kano

Ya ci gaba da cewa, a halin yanzu gwamnatin shugaba Buhari ta dukufa wajen tsarkake kasar nan daga dukkan wani nau'i na gurbata saboda haka dole a zuba idanu har sai ya kai kasar nan ga gaci.

Ya kara da cewa, soyayyar shugaba Buhari na ci gaba da gudana a zukatan masu kishin kasar nan ne da a halin yanzu sun daura damarar ganin ya yi tazarce a zaben 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel