Na kusa da Buhari na Matsa Masa Lamba akan ya Mayar da Lawan Daura shugaban DSS

Na kusa da Buhari na Matsa Masa Lamba akan ya Mayar da Lawan Daura shugaban DSS

Sanata Dr. Junaid Mohammed, ya bayyana cewa akwai kishin kishin dake nuna cewa dama can akwai wata kaykkyawar dangantakar siyasa tsakanin tshohon shugaban hukumar tsaro ta fararen kaya DSS, Lawan Daura, da shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki.

Dangin Buhari na Matsa Masa Lamba akan ya Mayar da Lawan Daura shugaban DSS

Dangin Buhari na Matsa Masa Lamba akan ya Mayar da Lawan Daura shugaban DSS

Sanata Junaid Mohammed, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai, dangane da yadda yake kallon kutsen da hukumar DSS tayiwa Majalisar Dokoki ta kasa a makwannin da suka wuce.

Yana mai cewa tuni suke zargin tsohon shugaban hukumar da kin tabbatar da biyayyarsa ga shugaban kasa, mataimakinsa, dama majalisar dokoki ta kasar.

KU KARANTA: Mutane Miliyan Biyu ne Ake Saran Zasuje Aikin Hajjin Bana - Hukumar Saudi

"Awai kishin kishin dake nuni da cewa shi (Lawan Daura) yana da kyakkyawar alakar siyasa tsakaninsa da shugaban majlisar dattawa Bukala Saraki. Ko da yake, indai a Nigeria kake to zaka rinka cin karo da abubuwan ban mamaki a kowace rana saboda akwai ma'aitan dake aiki da zuciya biyu, kuma ire iren wadannan mutanen ne ke sayar da yancinsu." A cewarsa.

Dr. Junaid Mohammed ya ce: "Dole ne mutum yayi taka tsan-tsan wajen yanke hukuncin ainihin abunda ya faru, da wanda bai faru ba, dama wanda zai faru nan gaba. Idan aka duba cece kuce kan kutsen da akayiwa majalisar dokoki, akwai sanatoci a cikin ginin, shin za'a ce mutanen nan sune suka shiga suka zauna suka ce "Ku kullemu?". Tambayar a nan itace; idan har da ana so ne a hana kowa shiga, to taya har wasu suka samu hanyar shiga ciki har suka samun wuri suka zauna?"

"Tun bayan faruwar lamarin, har zuwa korar Lawan Daura dama kamashi da akayi, babu wani jawabi daga bakin Buhari, kawai dai cece kuce ake. Akwai ma majiyar data ce Yemi Osinbajo ya cire Lawan Daura daga mukamin shugabancin hukumar DSS da sanin Buhari"

Ko da aka tambayi Sanata Dr. Junaid Mohammed, dangane da batun matsain lambar da akewa shugaba Buhari don ya mayar da Lawan Daura a bakin aiki, Dr. Junaid yace: "Akwai dangin Buhari, wadanda suma dangin Lawan Daura ne, mutanen Daura, sun je har Burtaniya inda Buhari yake , suka bukace shi da ya maido Lawan Daura yaci gaba da aiki, kana ya kori mai tallafa masa ta fuskar harkokin tsaro, wanda suke yar tsama da Lawan Daura"

Dangane da sabon shugaban Jam'iyar APC kuwa, Sanata Junaid ya ce baya tunanin Oshimohle nada kwarewar da zai yi jagorancin jam'iyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel