Shugaba Buhari ya yabawa sauyin shekar Akpabio yayi bakam da batun Saraki

Shugaba Buhari ya yabawa sauyin shekar Akpabio yayi bakam da batun Saraki

Kun ji labari cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dawo gida Najeriya bayan wani ‘dan hutu na kusan makonni 2 da yayi a kasar Ingila. Shugaban kasar yayi hira da ‘Yan jarida bayan ya dawo don haka mu ka kawo kanun abin da ya fada:

Shugaba Buhari ya yabawa sauyin shekar Akpabio yayi bakam da batun Saraki

Shugaba Buhari yace 'Yan Najeriya su zabi wanda su ke so a 2019

Daga cikin abin da Shugaba Buhari ya fada a fadar Shugaban kasa a jiya akwai:

1. Batun kama barayin kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara yin kira da babbar murya cewa zai yi ram da barayin Najeriya wadanda su ka saci kudi su ka kuma kashe tattalin arzikin kasar nan kwanan nan. Shugaba Buhari yace ‘Yan kasar ma na sa ran yayi hakan.

KU KARANTA: Buhari yayi wayar tarho da wani Gwamnan Kudancin Najeriya

2. Sauya-shekar ‘Yan siyasa

A jiyan dai Shugaban kasa Buhari ya yabawa sauyin shekar da wasu manyan ‘Yan siyasar kasar irin su tsohon Gwamnan Akwa-Ibom Sanata Godswill Akpabio su kayi inda yace hakan na nuna cewa siyasar damukaradiyya rigar ‘yanci ce.

3. Shawara game da zaben 2019

Kusan dai Shugaban kasar ya wadanda su ka dawo APC shawara cewa su karfafa mutanen Yankin su sannan kuma su nuna masu muhimmancin samun katin zabe a 2019. Shugaba Buhari kuma ya nemi masu zabe su zabi ‘Yan takarar da su ke so a 2019.

Shugaban kasar dai yayi bakam game da batun takaddamar da aka samu tsakanin Jami’an tsaro da ‘Yan Majalisa bayan tafiyar sa. Shugaba Buhari dai kuma bai ce komai game da batun tsige Bukola Saraki ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Mailfire view pixel