Bikin Sallah: Gwamna Tambuwal ya yiwa marayun Sakkwato sha tara na arziki

Bikin Sallah: Gwamna Tambuwal ya yiwa marayun Sakkwato sha tara na arziki

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato ya rabawa masu hakimai 86 zunzurutun kudi N14.68 miliyan domin su siyawa marayu naman salla a jihar.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito cewa gwamnatin ta saba bayar da wannan tallafin duk shekara ta ofishin Zakka wanda aka kafa a fadar Sarkin Musulmi Sultan Abubakar Sa'ad III.

A yayin da ake kafa kwamitin, Sultan Sa'ad Abubakar III ya jinjinawa hakiman bisa irin jajircewa da goyon baya da suka bayar domin ganin shirin yana samun nasara a garuruwansu.

Bikin Sallah: Gwamna Tambuwal ya yiwa marayun jihar Sakkwato sha-tara na arziki

Bikin Sallah: Gwamna Tambuwal ya yiwa marayun jihar Sakkwato sha-tara na arziki

Sarkin musulmi ya ce shirin ya yi nasara sosai saboda yana taimakawa marayu wajen debe musu kewa da ganin cewa sunyi shagalin Sallah cikin murna da farin ciki kamar sauran jama'anm gari.

DUBA WANNAN: Matar aure ta mutu a dakin saurayinta bayan ta gama cin amanar mijinta

"Taimakawa marayu nauyi ne da ya ratayu a kan kowa da kowa saboda hakan akwai lada sosai daga wajen Ubangiji, ya kuma ce taimakon yana kawo cigaba a garuruwa.

"Saboda haka, ina kira ga dukkan wandanda aka daurawa nauyin suji tsoron Allah wajen gudanar da ayyukansu saboda su samu ladan gudanar da ayyukan," inji Sarkin Musulmi.

Sarkin musulmi ya mika godiyarsa ga gwamnatin jihar Sakkwato da hukumar Zaka na jihar Sakkwato saboda cigaba da gudanar da shirin.

Ya yi addu'an Allah ya taimakawa dukkan al'umman musulmi wajen gudanar da ibadunsu kuma ya bukaci su rika yiwa Najeriya addu'an samun zaman lafiya da cigaba.

Da farko, Ciyaman din kwamitin Zakat, na jihar, Lawal Madoki, ya ce shirin na cikin ayyukan gwamnatin jihar ya ce wannan sha-tara-na arzikin yana daya daga cikin yunkurin gwamnati don taimakawa marayu da marasa galihu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel