Dalilin da yasa ba za muyi hadin gwiwa da APC da PDP ba - ADP

Dalilin da yasa ba za muyi hadin gwiwa da APC da PDP ba - ADP

Ciyaman din Action Democratic Party (ADP), Yabagi Sani, ya ce jam'iyyarsu ta tsame hannunta daga yin wata hadin gwiwa da jam'iyyar APC da PDP ne saboda sun gano cewa kawai "barayin dukiyar gwamnati ke sake haduwa."

A yayin yake hira da manema labarai a wajen taron masu ruwa da tsaki a jam'iyyar na yankin Kudu maso Yamma da akayi a ranar Asabar a Legas, Sani ya bukaci a tsige dukkan 'yan majalisun tarayya.

Dalilin da yasa ba za muyi hadin gwiwa da APC da PDP ba - ADP

Dalilin da yasa ba za muyi hadin gwiwa da APC da PDP ba - ADP

"Mun janye daga hadin gwiwa da jam'iyyar PDP bayan mun lura cewa dukkan mutanen da suka sace kadaden Najeriya a baya ne ke sake haduwa duk da cewa jama'a sun nuna basu kaunarsu," inji Mr Sani.

DUBA WANNAN: Matar aure ta mutu a dakin saurayinta bayan ta gama cin amanar mijinta

"Munyi imanin cewa cigaban Najeriya shine abinda ya kamata a sanya a gaba, dole ne a gudanar da sahihiyar zabe kuma idan majalisar dattawa zata sake duban kasafin kudin INEC, tayi hakan ba tare da kawo siyasa ciki ba."

Mr Sani yace jam'iyyarsu da INEC ta yiwa rajista a shekarar 2017 zata hada kai da 'yan Najeriya masu nagarta don tunkarar jam'iyyar APC a babban zaben 2019 mai zuwa.

"Bamu neman mutanen da basu alfahari da Najeriya da kuma wadanda idanunsu ya rufe har ta kai basu aikata komai sai satar kudaden Najeriya,

"Duba irin mutanen da ke hadin gwiwa, duk cikinsu babu wanda 'yan Najeriya suka amince dasu domin duk ana zarginsu da handama. Muna neman 'yan Najeriya masu nagarta ne.

Mun kafa ADP ne saboda jama'an Najeriya ne bukatar jam'iyya mai nagarta kuma bisa ga dukkan alamu an fara ganewa cewa muna da nagarata. Dukkan sauran manyan jam'iyyun yanzu sun zama kwanko.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel