Bayan ya sauya sheka zuwa APC, PDP ne neman tsige Akpabio

Bayan ya sauya sheka zuwa APC, PDP ne neman tsige Akpabio

Jam'iyyar PDP reshen jihar Akwa Ibom ta rubuta wasika ga shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, inda take bukatar kwace kujerar Sanata Godswill Akpabio mai wakiltar Arewa maso Yammcin Akwa Ibom saboda ya sauya sheka zuwa APC.

Kafin sauya shekarsa zuwa jam'iyyar APC, Sanata Godswill Akpabio ne shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa.

Mr Ini Emembong, sakataren yadda labarai na jam'iyyar PDP reshen jihar Akwa Ibom, ya ce jam'iyyar ta cimma wannan matsayar ne saboda ta ce bata saba korar Sanatoci ba.

Bayan ya sauya sheka zuwa APC, PDP ne neman tsige Akpabio

Bayan ya sauya sheka zuwa APC, PDP ne neman tsige Akpabio

DUBA WANNAN: Matar aure ta mutu a dakin saurayinta bayan ta gama cin amanar mijinta

Emembong ya ce an rubuta wasikar ne ga shugaban majalisa Bukola Saraki saboda shine kadai yake da ikon annaya tumbeka Sanata a majalisar kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ta bashi iko.

Ya ce, "Za'a bayar da sanarwan ne a gaban majalisa. Mun nemi bukatan aikata hakan cikin wasikar ta muka rubuta. Bamu kai lamarin kotu ba saboda kundin tsarin mulki ya ce idan irin wannan abin ya faru, shugaban Majalisa ne ke da ikon tsige duk wanda ya canja sheka."

Anyi kokarin tuntubar Akpabio ta wayarsa na tarho amma wayar na kashe.

An kuma aika masa sakon kar ta kwana amma har lokacin da aka kammala wannan rahoton bai amsa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel